Majalisar Taraba ta kada kuri’ar yaba wa Mukaddashin Gwamnan Jihar
Majalisar Dokokin Jihar Taraba ta kada kuri’ar yaba wa Mukaddashin Gwamnan Jihar Alhaji Garba Umar kan kokarin da yake yi na maido da zaman lafiya tare da aiwatar ayyukan raya kasa a jihar. A wani zama na musamman da majalisar tab yi a shekaranjiya Laraba daukacin wakilan majalisar sun amince cewa Mukaddashin Gwamnan ya cancanci […]
Majalisar Dokokin Jihar Taraba ta kada kuri’ar yaba wa Mukaddashin Gwamnan Jihar Alhaji Garba Umar kan kokarin da yake yi na maido da zaman lafiya tare da aiwatar ayyukan raya kasa a jihar.
A wani zama na musamman da majalisar tab yi a shekaranjiya Laraba daukacin wakilan majalisar sun amince cewa Mukaddashin Gwamnan ya cancanci yabo kan himmar da ya nuna wajen maido da zaman lafiya a sassan da rikicin kabilanci da na addini ya shafa a ’yan watanin baya.
dan majalisa daga Mazabar Ibbi, Malam Abdulkarim Muhammed ne wanda ya gabatar da wani kudiri a majalisar inda ya nemi majalisar ta yaba da irin namijin kokarin da Mukaddashin Gwamnan yake yi wajen maido da zaman lafiya tare da aiwatar da ayyukan raya kasa a jihar.
Wakilan majalisar da dama sun yi bayyani kan kokarin Alhaji Garba Umar wajen dawo da zaman lafiya a jihar. Daga nan sai ’yan majalisar suka kada kuri’ar yaba wa Mukaddashin Gwamnan.
Da yake bayani ga manema labarai daga bisani, shugaban majalisar Mista Joshua Sabo Kente ya ce majalisar ta gamsu da namijin kokari da da Alhaji Garba Umar ya keyi wajen ingantar harkokin tsaro a jihar. Ya ce a yanzu haka gwamnatin jihar ta kafa wani kwamiti da zai sasanta al’ummar yankunan da rigingimun kabilanci da addini suka shafa da nufin yafe wa junansu don a samu dauwamammin zaman lafiya a yankunan.
Mista Sabo Kente ya ce zaman lafiya a sannu ya soma dawowa a wadannan yankuna, inda hukumar zabe ta kasa ta amince ta soma raba rajistar masu zabe a Kudancin Jihar da rikicin ya auku a watanin baya.
Shugaban ya ce kafa kwamitin da zai binciki gaskiyar lafiyar Gwamna danbaba Suntai da majalisar ta yi, ta yi shi ne a kan doka.
Ya ce tsarin mulkin kasar nan ne ya bai wa shugaban majalisa damar yin haka in an samu matsala ta rashin lafiyar Gwamna kamar yadda aka samu a Jihar Taraba.
Ya nuna bakin ciki kan yadda wasu suka cusa batun addini da kabilanci kan wannan lamari.Ya ce lamarin ba batun addini ne ba ne batu ne da ya shafi dokar kasa kuma dole ne a bi dokar kasa wajen warware shi.