Majalisar Tarayya ta dawo aiki
A yau Majalisar Tarayya za ta dawo bakin aiki bayan kwashe tsawon kwanaki suna hutu, duk da cewa yawancin ‘yan majalisa ba su shigo ba. Hakanan kuma wakilinmu ya ruwaito cewa an samu canjin jami’an tsaro da suke majalisar, sannan kuma an samu karin jami’an tsaron. Tun dai ranar 24 ga watan Yuni ne majalisar […]
Majalisar Dokokin Tarayya
A yau Majalisar Tarayya za ta dawo bakin aiki bayan kwashe tsawon kwanaki suna hutu, duk da cewa yawancin ‘yan majalisa ba su shigo ba.
Hakanan kuma wakilinmu ya ruwaito cewa an samu canjin jami’an tsaro da suke majalisar, sannan kuma an samu karin jami’an tsaron.
Tun dai ranar 24 ga watan Yuni ne majalisar ta fara hutu bayan wasu daga cikin sanatoci da ‘yan majalisar wakilai sun canja sheka zuwa PDP.