Majalisar Tarayya ta ki yarda a dandake masu fyade
Majalisar Wakilai ta yi watsi da kiran da aka yi na zartar wa wadanda aka samu da laifin fyade hukuncin dandaka. Majalisar ta dauki matakin ne ranar Alhamis bayan kiraye-kirayen da aka yi sakamakon yawaitar rahotannin fyade da ake samu a Najeriya. Za a rataye wanda ya kashe ’yar shekara 3 ta hanyar fyade Matashi […]
Majalisar Wakilai ta yi watsi da kiran da aka yi na zartar wa wadanda aka samu da laifin fyade hukuncin dandaka.
Majalisar ta dauki matakin ne ranar Alhamis bayan kiraye-kirayen da aka yi sakamakon yawaitar rahotannin fyade da ake samu a Najeriya.
- Za a rataye wanda ya kashe ’yar shekara 3 ta hanyar fyade
- Matashi ya yi wa tsohuwa ‘yar shakera 70 fyade
Hakan ne ya sa dan majalisa James Faleke ya bukaci a yi dokar dandaka ko fidiye masu aikiata fyade a kasar.
Da yake mayar da martani a kan kudirin, Shugaban Majalisar Femi Gbajabiamila ya tambayi Faleke cewa. “Su kuma matan da suka yi wa mazan da suka fi karfi fyade wane hukunci za a yi musu?”
Wannan batu ya janyo ka-ce-na-ce a majalisar.