Majalisar Ukraine ta amince da sabuwar gwamnati
Sai dai amincewar ba ta haɗa da Ministocin tsaro da harkokin wajen ƙasar ba, domin bisa kundin tsarin mulkin Ukraine, shugaban ƙasa ne ke naɗa su.
Majalisar Dokokin Ukraine ta amince da kafa sabuwar gwamnati ƙarƙashin jagorancin sabon Firaminista, Sergii Koretskyi a wani mataki na sake fasalin gwamnatin ƙasar yayin da take ci gaba da fuskantar yaƙi da Rasha.
Sai dai amincewar ba ta haɗa da Ministocin tsaro da harkokin wajen ƙasar ba, domin bisa kundin tsarin mulkin Ukraine, shugaban ƙasa ne ke naɗa su.
Sabuwar gwamnatin na fuskantar ƙalubalen ci gaba da yaƙi, farfaɗo da tattalin arziki da kuma ƙarfafa alaƙa da ƙawayen ƙasar.
Kafin amincewar majalisar, Shugaban Ƙasar Ukraine, Volodymyr Zelensky ne ya zaɓi Koretskyi domin jagorantar sabuwar gwamnatin, a wani yunƙuri na sake fasalin shugabanci yayin da yaƙin da Rasha ke yi wa ƙasar ya shiga wani sabon yanayi.
Ana sa ran sabuwar gwamnatin za ta mayar da hankali wajen ƙarfafa tattalin arzikin ƙasar, bunƙasa masana’antar tsaro da kuma ci gaba da samun goyon bayan ƙasashen Yamma domin taimaka wa Ukraine a yaƙin da take yi da Rasha.