Majalisar Wakilai ta amince da ƙudirin dokar haraji
An dai shafe watanni ana taƙaddama kan dokar harajin wadda daga bisani gwamnonin jihohi 36 na Nijeriya suka cimma matsaya a kai.

Majalisar Wakilai ta amince da ƙudirin dokar haraji bayan ya tsallake karatu uku a wannan Talatar.
Wannan na zuwa ne bayan karatun tsanaki da majalisar ta yi ƙudirin a ranar Alhamis ta makon jiya.
- Wike ya ƙwace filin Sakatariyar PDP da ke Abuja
- Janar Tsiga ya shafe kwanaki 40 a hannun masu garkuwa duk da biyan kuɗin fansa
Ana iya tuna cewa, a makonnin bayan nan ne kwamitin kuɗi na majalisar ya gudanar da sauraron ra’ayin jama’a kan ƙudirin, inda kuma ya tattara ra’ayoyin al’umma ya miƙa wa majalisar.
Dokar harajin da majalisar ta amince da ita ta ƙunshi ƙudiri guda huɗu da suka haɗa da ƙudirin dokar tafiyar da haraji da na kafa hukumar tattara haraji mai suna Nigeria Revenue Service da hukumar haɗaka ta tattara haraji da kuma ƙudirin haraji na Najeriya.
A watan Okotoban bara ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aike da ƙudirin dokar ga majalisar dokokin ƙasar.
An dai shafe watanni ana taƙaddama kan dokar harajin wadda daga bisani gwamnonin jihohi 36 na Nijeriya suka cimma matsaya tare da amincewa da ƙudirin sabuwar dokar haraji, bayan gyare-gyaren da aka yi a kan rabon harajin kayayyaki na VAT da ya tayar da kura a ƙasar.