Majalisar wakilai ta amince da dokar ta-ɓaci a Ribas

Majalisar ta amince ne ta hanyar kaɗa ƙuri’a da baki, wanda ’yan majalisa 243 suka halarta.

Majalisar wakilai ta amince da dokar ta-ɓaci a Ribas

Majalisar Wakilai ta amince da ayyana dokar ta-ɓaci da Shugaba Bola Tinubu ya yi a Jihar Ribas.

Majalisar ta yanke wannan shawara ne a ranar Alhamis, ta hanyar kaɗa ƙuri’a da baki, inda ’yan majalisa 243 suka halarta.

A matsayin wani ɓangare na matakan dokar ta-ɓaci, majalisar ta bayar da shawarar kafa kwamiti domin dawo da zaman lafiya a jihar.

Hakazalika, majalisar za ta karɓi ragamar gudanar da ayyukan Majalisar Dokokin Jihar Ribas na tsawon watanni shida.

Me Ya Sa Aka Ayyana Dokar Ta-ɓaci?

Matakin ya biyo bayan rikicin siyasa da ya ƙi ya ƙi cinyewa a Jihar Ribas.

Shugaba Tinubu ya yanke wannan shawara ne sakamakon tashe-tashen hankula da rikicin shugabanci a jihar.

Gwamna Siminalayi Fubara na takun-saƙa da Majalisar Dokokin Jihar da wasu jiga-jigan ’yan siyasa musamman waɗanda ke tsagin tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike, lamarin da ya jefa jihar cikin tashin hankali.

Domim shawo kan matsalar, Tinubu ya naɗa Tsohon Babban Hafsan Rundunar Sojin Ruwa, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), a matsayin sabon mai kula da jihar.

Hakan ya sa Gwamna Fubara da wasu manyan jami’ai, ciki har da iyalansa, suka bar gidan gwamnatin jihar.

Ana ci gaba da sa ido kan halin da ake ciki a jihar, yayin da gwamnati ke ƙoƙarin tabbatar da doka da oda a jihar.