Majalisar Wakilai ta amince da muhimman kudirori 19 a zama daya
Majalisar Wakilai ta amince da wasu muhimman kudirori 19 a zamanta na ranar Alhamis din makon jiya a kokarinta na inganta gudanar da ayyukanta da kuma rage dogon lokacin da ake dauka wajen amincewa da kudirorin.Kakakin Shugaban Majalisar Wakilai, Turaki Hassan, ya fadi a wata sanarwar cewa kudiroin wadanda suke bukatar amincewar Majalisar Dattawa da […]
Majalisar Wakilai ta amince da wasu muhimman kudirori 19 a zamanta na ranar Alhamis din makon jiya a kokarinta na inganta gudanar da ayyukanta da kuma rage dogon lokacin da ake dauka wajen amincewa da kudirorin.
Kakakin Shugaban Majalisar Wakilai, Turaki Hassan, ya fadi a wata sanarwar cewa kudiroin wadanda suke bukatar amincewar Majalisar Dattawa da kuma lamuncewar Shugaban kasa, sun shafi muhimman bangarorin da suke bukatar kulawar wannan gwamnati da suka hada da yaki da cin hanci da rashawa da mafi karancin albashi na kasa da na kanana da matsakaitan masana’antu da bangarin kamfanoni da sauransu.
Idan za a iya tunawa a kwanakin baya majalisar ta amince da kudirori 130 ta hanyar karatun farkoa rana daya.
Wasu daga cikin kudirorin dokar da aka amince da su sun hada da gyararriyar dokar yaki da tu’annati ga tattalin arziki da gyararriyar dokar yaki da miyagun kwayoyi da kudirin dokar gyara dokar asusun bayar da rancen noma da kudirin gyara dokar yaki dacin hanci da rashawa da dokar daidaita ma’anar banki da cibiyoyin kudi da kuma sake fasarin yadda ake nada shugabannin hukumomi da daidaita wa’adin wakilan hukumomin.
Sauran kudirorin da aka amince da su sun hada da dokar kafa Hukumar Kare Yara ta kasa da kudirin gyara dokar hukumar kula da kanana da matsakaitan masana’antu da kudirin gyara dokar kara harajin kayan alatu da tara da hukuncin laifuffukan da suke karkashin dokar.
Wani muhimmin kudiri da majalisar ta amince da shi, shi ne kudirin dokar daidaita ’yanci da hakkokin yarjejeniyar haya da dangantakar da ke tsakanin dan haya da mai gidan haya ciki har da hanyar kwato muhalli a yankin Birnin Tarayya, Abuja da sauran batutuwan da suka shafi haka.