Majalisar Wakilai ta ba da umarnin rufe shafukan intanet na batsa
Kallon bidiyon batsa na da mummunan tasiri, ciki har da yiwuwar kusantar zina, da karuwanci, da kuma kasa rabuwa da kallon ta.

Zauren Majalisar Wakilai
Majalisar Wakilai ta bai wa Hukumar Sadarwa ta NCC umarnin rufe duk wasu shafukan intanet masu nuna batsa a Nijeriya.
Majalisar ta ba da wannan umarni yayin zamanta na yau Talata, inda ta nemi hukumar sadarwar ta umarci duk kamfanonin da ke samar da intanet su rufe duk wasu shafukan intanet da ke nuna hotuna ko bidiyon batsa cikin gaggawa.
Wannan umarni na zuwa ne bayan wani ƙudiri da ɗan majalisa daga Jihar Katsina, Dalhatu Shehu Tafoki, ya gabatar.
Tafoki ya bayyana cewa bidiyoyin batsa da ke intanet na zama babbar matsala a duniya, kuma zuwa yanzu Nijeriya ba ta ɗauki wani matakin magance matsalar ba.
Ya kafa hujjar cewa Nijeriya ƙasa ce mai addini, inda manyan addinan ƙasar suka haramta batsa da kuma nuna tsiraici.
Tafoki ya kuma bayyana gargaɗin da masana halayyar ɗan Adam suka yi kan mummunan tasirin da kallon bidiyon batsa ke da shi, ciki har da yiwuwar kusantar zina, da karuwanci, da kuma kasa rabuwa da kallon.
Majalisar ta kuma buƙaci hukumar NCC ta hukunta duk kamfanin samar da intanet da ya bijirewa wannan umarnin.