Majalisar Wakilai ta ba waɗanda Ambaliyar Maiduguri ta shafa 100m
Tawaga ta musamman ta Majalisar Wakilai ta ba wa al’ummar da ambaliyar Maiduguri ta shafa gudunmawar miliyan 100
Wata tawaga ta musamman ta Majalisar Wakilai ta ziyarci Maiduguri inda ta jajanta wa gwamnati da al’ummar Jihar Borno kan bala’in ambaliyar ruwa da ya addabi yankin.
Tawagar dai ta samu jagorancin tsohon shugaban masu rinjaye kuma shugaban ’yan Arewa a majalisar, Alhassan Ado Doguwa.
Doguwa ya ce a madadin shugaban majalisar, Tajuddeen Abbas da daukacin ’yan majalisar suka bayar da gudunmawar Naira miliyan 100 domin tallafa wa mutanen da ambaliyar ta shafa.
“Mun kuma yi alkawatin shirin majalisar na haɗa kai da Gwamnatin Tarayya don samar da tsarin doka ko duk wani abu da zai iya sa a yi kasafin kudi don taimaka wa gwamnatocin jihohi don magance illar bala’in ambaliyar ruwa a kasar nan,” inji shi.
- Sojoji sun kashe ’yan bindiga 4 sun ceto mutane 20 a Kaduna
- Kamaru ta buɗe Madatsar Lagdo: Jihohin 11 Najeriya su shirya wa ambaliya —Gwamnati
Tawagar ta ziyarci Shehun Borno a fadarsa inda ta jajanta masa bisa asarar rayukan da aka samu a lokacin bala’in ambaliyar ruwan.
Ya yaba wa shugaban kasa Bola Tinubu kan yadda ya ɗauki matakin gaggawa kan halin da al’ummar jihar Borno ke ciki ta hanyar tabbatar da goyon bayan gwamnatin tarayya ga gwamnatin jihar da wadanda abin ya shafa wajen gaggauta kai ziyarar gani da ido.