Majalisar wakilai ta dakatar da CBN daga ƙara kuɗin cajin ATM

Majalisar ta ce sabon tsarin zai ƙara jefa ‘yan Najeriya cikin tsanani.

Majalisar wakilai ta dakatar da CBN daga ƙara kuɗin cajin ATM

Majalisar Wakilai ta umarci Babban Bankin Najeriya (CBN), da ya dakatar da sabon tsarin ƙarin caji kan cire kuɗi ta na’urar ATM.

Wannan umarni ya biyo bayan wata sanarwa da CBN ya fitar, inda ya ƙuduri aniyar fara cajin Naira 100 kan duk cire Naira 20,000 daga ATM a banki, daga ranar 1 ga watan Maris, 2025.

Ɗan majalisa Marcus Onobun (PDP, Edo) ne, ya jagoranci ƙudirin da ya buƙaci a dakatar da wannan tsari, inda ya bayyana cewa tsarin zai ƙara jefa ’yan Najeriya cikin wahala.

Ya bayyana cewa, a shekarar 2019, an rage cajin cire kuɗi ta ATM daga Naira 65 zuwa Naira 35, don sauƙaƙa wa al’umma.

Sabon tsarin na CBN ya tanadi cewa, idan kwastoma ya cire kuɗi daga ATM na bankinsa, ba za a caje shi komai ba; amma idan ya cire daga ATM na wani banki daban, za a caje shi Naira 100 kan kowace Naira 20,000 da ya cire.

Majalisar ta nuna damuwa cewa wannan ƙarin caji zai ƙara matsin lamba ga ‘yan Najeriya, musamman ma masu ƙaramin ƙarfi, waɗanda ke fama da hauhawar farashin kayayyaki da sauran matsalolin tattalin arziƙi.

Saboda haka, ta umarci CBN da ya dakatar da aiwatar da wannan sabon tsari har sai an gudanar da cikakken nazari tare da tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin samun mafita mai ɗorewa.

Majalisar wakilai ta dakatar da CBN daga ƙara kuɗin cajin ATM

Hanyoyi 6 da mutum zai kare kansa daga tsananin zafi

’Yan sanda sun ceto mutum 30 daga hannun ’yan bindiga a Katsina

Ba abin da zai faru idan aka tsige Fubara – Wike