Majalisar Wakilai ta musanta karɓar kuɗi kan dokar ta-ɓaci a Ribas

Ɗan majalisar ya ce babu wanda ya tilasta musu domin amincewa da dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas.

Majalisar Wakilai ta musanta karɓar kuɗi kan dokar ta-ɓaci a Ribas

Majalisar Wakilai ta ƙaryata zargin da ake mata na karɓar cin hanci domin amincewa da dokar ta-ɓaci da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ayyana a Jihar Ribas.

Ɗan majalisa mai wakiltar mazabar Gwaram a Jihar Jigawa, Hon. Yusuf Shittu Galambi, ya kare majalisar yayin da ake ta cece-kuce kan batun.

Wasu ƙungiyoyi na zargin majalisar da yin ƙasa a gwiwa wajen yanke hukunci kan lamarin.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, Galambi, ya ce babu gaskiya a zargin da ake yi cewa an tursasa ’yan majalisa ko an ba su na goro don su amince da matakin shugaban ƙasa.

Ya bayyana cewa yawancin mambobin majalisar sun goyi bayan matakin ne domin kare dimokuraɗiyya da kuma tsare muradun al’ummar Jihar Ribas.

“Mun yanke shawarar ne bisa kishin ƙasa, haɗin kan siyasa, zaman lafiya, da kare dimokuraɗiyya,” in ji shi.

Ya ce ya yi mamakin yadda wasu kafafen yaɗa labarai ke baza jita-jita cewa an tilasta musu su amince da dokar ta-ɓaci tare da karɓar daloli.

A cewarsa, ya kamata ’yan Najeriya su fahimci cewa ’yan majalisa suna aiki ne don ganin an samar da tawagar sulhu kafin wa’adin dokar ta-ɓacin ta ƙare.

Ya jaddada cewa dole ne a kare dimokuraɗiyya a Najeriya.