Majalisar Wakilai ta nemi gwamnati ta gaggauta dauko Jonathan daga Guinea Bissau

Majalisar Wakilai a ranar Alhamis, ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta yi amfani da diflomasiyya da duk wasu hanyoyi don tabbatar da dawowar tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan lafiya daga Guinea Bissau, bayan juyin mulkin sojoji a ƙasar. 

Majalisar Wakilai ta nemi gwamnati ta gaggauta dauko Jonathan daga Guinea Bissau

Majalisar Wakilai a ranar Alhamis, ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta yi amfani da diflomasiyya da duk wasu hanyoyi don tabbatar da dawowar tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan lafiya daga Guinea Bissau, bayan juyin mulkin sojoji a ƙasar. 

Wannan kuduri ya biyo bayan amincewa da kudurin gaggawa da Shugaban Masu Rinjaye na majalisar, Farfesa Julius Ihonvbere, ya gabatar.

Ihonvbere ya shaida wa Majalisar cewa Jonathan, wanda ya je ƙasar domin sa ido kan zaɓe, ya makale bayan juyin mulkin, yana mai cewa gwamnati ta nemo hanyoyin da za su tabbatar da dawowarsa lafiya.

Tsohon shugaban Najeriya tare da daruruwan masu sa ido na ƙasashen waje sun makale a ranar Laraba bayan sojoji sun yi juyin mulki a lokacin da ake shirin bayyana sakamakon zaɓe.

Rahotanni sun ce daruruwan masu sa ido na ƙasashen waje da suka garzaya filin jirgi domin barin ƙasar bayan sanarwar juyin mulki, amma yanzu haka sun makale a can.

Wata ƙungiyar hafsoshin sojoji ta bayyana cewa ta karɓi cikakken iko da mulkin ƙasar, kwana guda bayan manyan ’yan takara biyu, Shugaba Umaro Sissoco Embalo da Fernando Dias, kowannensu ya yi ikirarin samun nasara.

Sojojin sun bayar da umarnin dakatar da tattara sakamakon zaɓen har sai an ba da sanarwa ta gaba.

Haka kuma sun bayar da umarnin rufe dukkan iyakokin ƙasa da na sama da ruwa, tare da sanya dokar hana fita da dare.

“An yin min juyinmulki,” in ji Embalo a zantarwarsa da gidan talabijin na Faransa France24 ta wayar tarho, yana mai cewa “yanzu haka ina hedkwatar babban hafsan sojoji.”

Shugaban babbar jam’iyyar adawa ta PAIGC, Domingos Simoes Pereira, ma an kama shi, in ji Haque. “Haka kuma mun ji cewa sojoji na ƙoƙarin katse intanet. An kuma sanya dokar hana fita.”

Shugaban rundunar tsaron fadar shugaban ƙasar, Denis N’Canha, shi ne dai sojan da ke jagorantar juyin mulkin.