Majalisar Wakilai za ta binciki dambaruwar Super Eagles a Libya
Tawagar ‘yan wasan sun sauka a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano a ranar Litinin.
Majalisar Wakilai ta umarci kwamitocinta na Wasanni da Harkokin Waje su binciki dalilin sa ya sa aka wulaƙanta tawagar ƙwallon ƙafa ta Najeriya, a ƙasar Libya.
Majalisar ta yi Allah wadai da irin yanayin da tawagar ’yan wasan suka fuskanta Libya.
- Gwamnatin Libya ce ta hana Super Eagles sauka a Benghazi —Matukin Jirgi
- Tsadar abinci ta karu zuwa 37.8% a Najeriya
Kazalika, majalisar ta buƙaci Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya (NFF) da ta gabatar da ƙorafi ga CAF da FIFA don su gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
Wannan umarni ya biyo bayan wani kudiri da ɗan majalisa Kabiru Ahmadu ya gabatar.
Aminiya ta ruwaito yadda Super Eagles suka sauka a Filin Jirgin Saman Malam Aminu Kano a ranar Litinin.
Yanzu haka tawagar na jiran sakamakon binciken da CAF za ta gudanar.
’Yan wasan Najeriya da tawagarsu sun maƙale a Filin Jirgin Albraq na Libya tsawon sama da sa’o’i 16 ba tare da ba su damar shiga otal ko amfani da Intanet ba.
Wani ɗan majalisa, Chris Nkwonta, ya bayyana cewa yadda aka yi wa tawagar rashin adalci abin kunya ne ga Najeriya da Afirka baki ɗaya.
Ya jaddada buƙatar gudanar da bincike cikin gaggawa don gujewa faruwar hakan a gaba.