Majalisar Wakilan Amurka ta tsige Shugaba Trump

Majalisar Wakilan Amurka ta jefa kuri’ar tsige Shugaban Kasar Donald Trump, bisa wasu laifuffuka guda biyu da ta same shi da su. Shugabar Majalisar, Nancy Pelosi ta ce ’yan majalisa 230 sun goyi bayan tsige Shugaban yayin da 197 suka ki amincewa. Laifin Mista Trump na farko shi ne kokarin tursasa Shugaban Ukraine ya binciki […]

Majalisar Wakilan Amurka ta tsige Shugaba Trump

Shugaba Donald Trump na kasar Amurka

Majalisar Wakilan Amurka ta jefa kuri’ar tsige Shugaban Kasar Donald Trump, bisa wasu laifuffuka guda biyu da ta same shi da su.

Shugabar Majalisar, Nancy Pelosi ta ce ’yan majalisa 230 sun goyi bayan tsige Shugaban yayin da 197 suka ki amincewa.

Laifin Mista Trump na farko shi ne kokarin tursasa Shugaban Ukraine ya binciki abokin hamayyarsa a zabe mai zuwa, kuma tsohon Mataimakin Shugaban Kasar,  Joe Biden.

Laifi na biyu  ya hada da kokarin kawo wa majalisa tarnaki, Mista Trump ya zamo shugaba na uku da aka taba tsigewa a tarihin Amurka.

A yanzu kallo zai koma Majalisar Dattawa da ’yan Jam’iyyar Republican ta Shugaban ke da rinjaye domin bincikarsa.

Masana na ganin zai yi wuya su amince da wannan mataki na Majalisar Wakilai.

Shi kuwa Shugaba Trump ya mayar da martani ne a wani gangami a Michigan, yana nuni da cewa ko a jikinsa:

“Ya ce na fada a wasikata da na aike wa Pelosi cewa, ci gaba da shirinki na tsigewar da ba ta da amfani, kina saba rantsuwarki ta aiki, kina saba biyayyarki ga tsarin mulki, kin kaddamar da yaki a kan dimokuradiyyar Amurka,” kamar yadda BBC ya ruwaito.