Majalisar za ta ceto ma’aikatan kananan hukumomin Nasarawa
Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa ta umurci shugabannin kwamitocinta na kudi da na harkokin kananan hukumomi su gayyaci masu hannu a kin biyan ma’aikatan kananan hukumomin jihar albashinsu, don su bayyana dalilin rashin biyan.Umurnin ya biyo bayan wani kudiri ne da Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye, Ogbere Kana ya gabatar game da sakacin da ake yi da […]
Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa ta umurci shugabannin kwamitocinta na kudi da na harkokin kananan hukumomi su gayyaci masu hannu a kin biyan ma’aikatan kananan hukumomin jihar albashinsu, don su bayyana dalilin rashin biyan.
Umurnin ya biyo bayan wani kudiri ne da Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye, Ogbere Kana ya gabatar game da sakacin da ake yi da harkokin kananan hukumomin jihar.
Ogbere Kana ya ce harkokin kananan hukumomi suna fuskantar koma-baya a halin yanzu sakamakon rashin tallafin kudi da gwamnatin jihar ba ta ba su tare da rashin adalcin shugabannin kananan hukumomin, inda ya yi kira ga gwamnatin ta rika taimaka wa kananan hukumomi don ceto su daga halin rashin kudi.
Da suke ba da nasu gudunmawa Babban Mai tsawatarwa, Malla Makpa da mambobi masu wakiltar Lafiya ta Tsakiya Abubakar Zanuwa da na Akwanga ta Kudu Kasim Muhammed Kasim sun ce dole ne shugabannin kwamitocin biyu su yi aiki tare don tabbatar da an magance lamarin cikin gaggawa kasancewar ma’aikatan na fama da wahala sakamakon rashin biyansu albashinsu na wasu watanni.
A jawabin Shugaban Majalisar Balarabe Ibrahim Abdullahi ya ce jama’a da dama daga kananan hukumomi suna kiransa ta waya kullum dangane da batun rashin biyan ma’aikatan albashinsu na wasu watanni. Saboda haka a cewarsa dole ne majalisar ta hada hannu da gwamnati wajen magance lamarin.