Majalisar za ta saya wa sanatoci motocin alfarma na kusan Naira biliyan 5
Duk da matsalar karancin kudi da kasar nan ke fama da ita, Majalisar Dattawa ta yanke matsayar saya wa sanatoci motocin alfarma na Naira biliyan hudu da miliyan 700, inda za a saya wa Shugaban majalisar Bukola Saraki da Mataikinsa motoci goma-goma.Wadannan motoci da za a saya wa sanatocin an kiyasta za su lashe wannan […]
Duk da matsalar karancin kudi da kasar nan ke fama da ita, Majalisar Dattawa ta yanke matsayar saya wa sanatoci motocin alfarma na Naira biliyan hudu da miliyan 700, inda za a saya wa Shugaban majalisar Bukola Saraki da Mataikinsa motoci goma-goma.
Wadannan motoci da za a saya wa sanatocin an kiyasta za su lashe wannan kudi da idan da za a yi amfani da su wajen yin allurar rigakafi ga jarirai da an ceto rayukansu, ko a samar da wutar lantarki ga al’ummomin karkara.
A daidai lokacin da ake yunkurin sayen motocin, al’ummar kasar nan na fama da dogon layin mai, saboda gwamnati ta kasa biyan masu shigo da man biliyoyin Naira da suke bin ta na kudin tallafi.
Kuma sanatoci na bukatar motocin su kasance wadanda za a yi yayinsu a badi kuma kirar Amurka masu na’urorin juya akala, yadda za a ji dadin sarrafa su. Tuni dai majalisar ta bayar da tallar neman wadanda za su sayo motocin a jaridu. Nau’ukan motocin sun hada da kirar Amurka b8, bdR, 5.7
Masana sun soki lamirin yunkurin sayen motocin da ’yan majalisar ke nufin yi, musamman ganin cewa da kudin da suke nufin warewa za a iya gina gidaje 671 a kan Naira miliyan bakwai kowanensu, sannan za a iya samar wa iyalan da ke zaune a gidaje dubu 51 ruwan famfo a kan Naira 92. Kuma masanan sun yi kiyasin cewa, za a iya samar da kujeru da teburtan karatu a makarantu har dubu 470, a kan Naira dubu 10 kowanensu. To sai a yi tunani ganin yadda yara ke koyon karatu a kan daben kasa a makarantu da dama.