Majalisar Zamfara ta gabatar wa Gwamna Yari kwamishinonin da aka tantance
Majalisar Jihar Zamfara karkashin jagorancin, shugaban majalisa Sanusi Garba Rikiji, ta mika wa gwamnan jihar sunayen kwamishinonin da suka tantance.Shugaban majalisar ya bayyana wa Gwamnnan AbdulAziz cewa, sunayen kwamishinonin da aka ba su domin tantancewa sun tsallake gaba dayansu, ya ce sun gamsu da zaben da gwamnan ya yi.Duk da shugaban majalisar ya bayyana cewa […]
Majalisar Jihar Zamfara karkashin jagorancin, shugaban majalisa Sanusi Garba Rikiji, ta mika wa gwamnan jihar sunayen kwamishinonin da suka tantance.
Shugaban majalisar ya bayyana wa Gwamnnan AbdulAziz cewa, sunayen kwamishinonin da aka ba su domin tantancewa sun tsallake gaba dayansu, ya ce sun gamsu da zaben da gwamnan ya yi.
Duk da shugaban majalisar ya bayyana cewa cikin ka’idodin da suka yi amfani da su gurin tantance kwamishinonin, akwai kwarewa a aiki da kuma tabbatar da cewa wanda za a tantancen yana da biyayya ga gwamnati da dai sauransu.
Gwamnan ya yi matukar farin ciki, kuma ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba za a rantsar da su, domin jihar ta tsaya daidai.
Ya ce duk da cewa kowa ya san halin da ake ciki, ya ce ko makancewa mutum ya yi ya san gaskiya, kuma kowa ya san ba haka aka fito ba. Don haka dole a yi hakuri, amma gwamnati za ta yi iyakacin kokarinta, kuma nan ba da jimawa ba gwamnatinsa za ta kama aiki gadan-gadan.