Majalisar Zartarwa ta amince a yi wa NYSC garambawul
Bayan fiye da shekara 50 ana ganin lokaci ya yi da za a sake duba manufofi da tsarin gudanar da shirin NYSC.
Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC), wadda ke ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ta amince a yi wa Hukumar Yi Wa Ƙasa Hidima (NYSC) garambawul.
Ministan Matasa, Ayodele Olawande, ne ya bayyana hakan bayan taron majalisar da aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a ranar Litinin.
- Sojoji sun ceto ɗalibai da malamai 10 da mayaƙan ISWAP suka sace a Borno
- Rikicin manoma da makiyaya ya jikkata mutum 12 a Kano
A cewarsa, sauye-sauyen za su haɗa da cikakken nazari kan tsarin NYSC domin ya dace da buƙatun Najeriya na wannan zamani.
A cewarsa, domin aiwatar da sauye-sauyen, majalisar ta umarci Babban Lauyan Tarayya da Ma’aikatar Matasa da su yi wa dokar NYSC da sauran dokokin da suka dace kwaskwarima domin samar da tubalin doka da ake buƙata.
Olawande ya ce sauye-sauyen za su mayar da NYSC wata hukuma da za ta fi mayar da hankali kan koyar da ƙwarewa da haɓaka samar da aiki, daidai da manufar Shugaba Tinubu ta gina tattalin arzikin Najeriya mai darajar dala tiriliyan ɗaya.
Daga cikin sauye-sauyen da aka amince da su akwai amfani da fasaha wajen tsarin kiran masu bautar ƙasa, tsarin tura masu yi wa ƙasa hidima bisa la’akari da matakan tsaro, da kuma sake fasalin shirin horaswa na makonni shida domin ƙara mayar da hankali kan shugabanci, kasuwanci, ƙwarewar fasahar zamani da hanyoyin bunƙasa sana’a.
Ministan ya ƙara da cewa za a riƙa bai wa masu yi wa ƙasa hidima wuraren aiki da suka dace da fannin karatunsu da kuma burinsu na sana’a.
Sauran sauye-sauyen sun haɗa da inganta sansanonin horaswa ta hanyar tsarin tantance inganci da bayar da takardar shaidar cancanta, ƙaddamar da sabon bikin kammala hidima da zai maye gurbin bikin faretin kammala hidimar na Passing Out Parade, da kuma sake fasalin kayan NYSC domin ƙara inganta ƙwarewa da alfaharin ƙasa.
Olawande ya bayyana cewa an fara aikin sake duba tsarin ne tun shekarar 2025 ta hanyar tattaunawa tsakanin Ma’aikatar Matasa, Ma’aikatar Ilimi da Ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Manufofi da Tsare-tsare, kafin Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince da shi.
Ya ce an dai assasa shirin NYSC ne a shekarar 1973 domin ƙarfafa haɗin kan ƙasa bayan Yaƙin Basasa, amma bayan fiye da shekara 50 ana ganin lokaci ya yi da za a sake duba manufofi da tsarin gudanar da shirin.