Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Shugaba Bola Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa a ranar Alhamis, 14 ga watan Nuwamban 2024.

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu yayin jagorantar taron Majalisar Zartarwa

Majalisar Zartarwa ta amince da daftarin Naira tiriliyan 47.9 a matsayin Kasafin Kuɗin Najeriya na 2025.

Ministan Kasafi da Tsare-Tsare Tattalin Arziki, Atiku Bagudu ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai bayan kammala zaman majalisar da Shugaba Bola Tinubu ya jagoranta.

A cewarsa, Majalisar ta sanya canjin dala a kan Naira 1400 haka nan ita kuma gangar man fetur a kan dala 75 yayin da za a riƙa haƙo gangan miliyan 2.06 ta ɗanyen man fetur duk rana a ƙasar.

Ministan ya ce la’akari da ƙaruwar kashi 3.19 cikin 100 na ƙarfin tattalin arzikin Najeriya a rubu’i na biyu na shekarar nan, Gwamnatin Tarayya za ta himmatu wajen daƙile hauhawar farashi tare da ɗaukar matakan da tattalin arzikin zai samu daidaito.

Ya ce tattalin arzikin Najeriya ya koma kan turbar da ta dace a yanzu, lamarin da zai sa ya ci gaba da bunƙasa.

Ministan ya kuma bayyana cewa majalisar ta yi bitar yadda ake aiwatar da Kasafin Kuɗin shekarar 2024, inda ya ƙara da cewa hakan ya haɗa da kyakkyawan ci gaba a fannin tattara kuɗaɗen shiga da hanyoyin kashe kuɗaɗen a wuraren da suka dace.

Yadda dagacinmu ya sassara ni da adda — Maraya

Bidiyoyin da suka ɗauki hankalin ’yan Najeriya a 2024

An kama mutum 859 da ceto 46 da aka yi garkuwa da su a Filato – ’Yan sanda

Sojoji sun kashe shahararren ɗan bindiga a Zamfara