Majalisar Zartaswa ta dage tattaunawa kan ƙarin mafi ƙarancin albashi
Ministan ya ce an bar wa Tinubu takardar kan sabon tsarin mafi ƙarancin albashi don yin nazari.
Majalisar Zartaswa ta Tarayya (FEC), ta jingine batun sabon mafi ƙarancin albashi zuwa wani lokaci.
Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris ne, ya shaida wa manema labarai, cewa abubuwa 39 na daga cikin ajandar da FEC ta tattauna kuma duka an ɗauke su.
Game da batun mafi ƙarancin albashi, ya ce akwai rahoton kwamiti uku wanda ya ƙunshi ƙananan hukumomi, jihohi, NLC/TUC da kuma gwamnatin tarayya.
Ya ce kwamitin uku ya gabatar da rahotonsa kuma akwai takarda game da hakan.
Sai dai ya ce majalisar ba za ta iya yanke hukunci a kai ba saboda lamarin ya shafi ƙananan hukumomi, jihohi, gwamnatin tarayya, kamfanoni masu zaman kansu da ƙungiyoyin ƙwadago.
Don haka, ya ce an jingine batun sabon mafi ƙarancin albashi, domin shugaba Bola Tinubu ya samu lokacin yin nazari kafin ya aike wa majalisar dokoki.