Majaujawar manhajar Makaransuwa (2)

Majaujawar manhajar makaransuwa, juyin salon takun tunkarar zamani ne da ke da kawalniya, inda ake BOBO DA kWAMBON BOKOKO, ba wai don laluben NA-KOKO kawai ba, har ma da lekawa LOKO-LOKO, mu farmaki masu DAKON DAKON MANGALAR AURA,  ta yadda al’umma za ta samu ta SARARA. MAJAUJAWAR MANHAJAR MAKARANSUWA, na bayar da damar harhada abubuwa, […]

Majaujawar manhajar Makaransuwa (2)

Majaujawar manhajar makaransuwa, juyin salon takun tunkarar zamani ne da ke da kawalniya, inda ake BOBO DA kWAMBON BOKOKO, ba wai don laluben NA-KOKO kawai ba, har ma da lekawa LOKO-LOKO, mu farmaki masu DAKON DAKON MANGALAR AURA,  ta yadda al’umma za ta samu ta SARARA.

MAJAUJAWAR MANHAJAR MAKARANSUWA, na bayar da damar harhada abubuwa, don jin dadin ’yanlelen uba da uwa da ake yi wa hasafin haruffa cikin kaffa-kaffa, don su ji dadin kai wa ilimi caffa, su hada hannu su tafa, har a dauka ana ciyar da su daddadar tuffa. Kyautatuwar al’amura za su sanya Maigari ya tallafa, ’yan birni su rankwafa, wajen kafa ’yar gwafa, sannan na karkara su hada karfin karafa wajen dinka wa ’ya’yan Baffa tufa, ta yadda adon-gari za su samu mayafi su yafa. Kada dai ku ce na cika tsirfa, ko rikicin tsufa kan matsalar da ba ta kai kan akaifa ba. Wasu kuwa sukan ce na zurfafa, amma nasan ban zafafa ba.

Koda an cimma manufar MAJAUJAWAR MANHAJAR MAKARANSUWA, abin tambaya a nan yaya za a yi gamarin al’umma da ’ya’yansu ke koyon watsattsake da buda wagagen littattafai a MAKARANLUMMA ke fama wajen laluben MAKAMA?

Samar da MANHAJA MARA HAJIJIYA za ta kai mu ga gacin gudun gajiya, ta yadda a kowane fanni ilimi ’yan dugwi-duwi su kasance masu cin gwagwabar garabasar gajiya, a ingantacciyar managarciyar Haurobiya.Kada mu yarda mu zama WARARIYAR KARSANA doron takun zamani, domin fafutikarmu ta zamo sama wa al’umarmu matsuuni a doron duniya ko da an kewaye da Danni.

Haurobiyawa ya kamata mu fasko cewa hidimar al’umma ce mafi a’ala, matukar anason daina lalala, don shawo kan masu kutungwila da gilla, da ke yi wa al’umma illa. Irin wadanda ke neman galasla don su dinka galleliyar galila.

’yan makaranta abin da nike ta hankoron nusar da mu shi ne, yadda kamfanonin kamfatar dukiya ke ikrarin  hidimar  kyautata rayuwar al’umma, sai na ga ya dace MAKARANSUWA su kuduri aniyar daukar dawainiyar marasa galihu a cikin al’umma, musamman ’ya’yan kutare da MAKAFI ko kolo da titibiri, don gwama su a cikin ajin ’yan lelen iya da baba.

Tunda tsarinmajaujawar manhajar makaransuwa shi ne daidai da kun zamani, sai a yi kokain fito da tsarin musayar dalibai a tsakanin MAKARUMMA ko MAKARANTALAWA da MAKARANSUWA. Ina ganin yadda za a cimma wannan manufa it ace, a hanyar daukar daainiya masu hazaka da zalaka a cikin al’umma, ba tare da la’akari da cewa WANE ne dan WANE. Domin yin hakan na da matukar  fa’ida, ta yadda za mu daina asarar masana fanoni, musamman a tsakanin AREWATAWA.

Kuma kungiyoyin al’umma su hada karfi da karfe wajen ganin sun dauki nauyin masu fafutikar koyon watsattsake a fannonin KIMIYYA da kERE-kERE, har ma da kirkire-kirkiren MOTORIDO DA BABURIDO DA SHORIDO-SHORIDO, amma ba masu shara kire karayar ZUkI-TA-MALLE-KAMA KARE KA HADA SHI DA ZOMO, don kada kullum a karke da tatsuniyar GIZO DA kOkI ko labarin kANZON KUREGE.

Lallai Gwamnatin Baban-burin-huriyya ta sanya tallafi a MAKARANSUWA, ta yadda ’yan matsabban da iyaye ke jinka wa masu  safarar ilimi zai yi kasa warwas, don kowa ya iya kai ’yan dugi-dugwi da ke tsalle-tsalle a fafajiyar gidansa. Sai kawai mu sami saukin horar da Direbobin Alli da dimbin kwararru a fannonin tarairayar harkokin rayuwar al’umma.

Ya zama dole a yi karatun ta-natsu, don maganin tsuwar tsutsu yayin da ake fama da harigidon tutsun aura, al’amarin da ke haifar da DAKON DAKON MANALAR AURA, mai a yunkura a zabura wajen kawar da dabarbarun miyagu da ke kawo wa al’umma tarnaki. Jajircewar jigata juhala da tabbatar da adala, zai bai wa masu tasowa a cikin al’umma yin JIMIRIN JAJIRCEWA A JAM’IN JAMA’A JAMI’AR JIMRAU, har su kakaba wa kurungunsu TAGIYAR TUNAU, tare da klauce wa MNTUWAR MANTAU, uwa-uba a yasar da MAKE-MAKEN MAKAU!

Haurobiya sana’ar na-duke ce mai yiwuwa don shawo kan tabahuwa

Aiwatar da managartan sare-tsaren gudanar Da rayuwar Haurobiyawa zai tabbata ne kawai idan an samu rukunin al’umma da suka jajirce  wajen kishin kasa, amma ba lalitarsu ba; a samu masu aiki tukuru da za a iya gani kuru-kuru, sabanin yadda ake alkawarta batutuwan kanzon kurege, har a karke da cin shiwar Malam, wai sunan wani gari, ‘ AJI ko ACI SHIRU,’ ko Gabagadin giringidimin gigiwar giwaye. Kai Haurobiyawa ma na da masaniya kan yadda wajen kula da ingancin uwar jikin al’umma aka aiwatar da tsarin SHARbAR SHAWARMAR SHIRWA SHIRU.

Lamari dai mafi alfanu da ya kamata a nusar da masu koyon watsattsake da buda agagen littattafai a wannan farfajiya a Dodorido da ke cikin Amintacciyar jaridar kasar Haurobiya ba a wuce a samar da daidaiton samun damar koyi ka koyar a tsakanin al’ummar kasa, ta yadda kowa zai samu alkiblar rayuwa, tare da shawo kan tsilli-tsillin matsalolin zaman-tattakewa da siyasar yasar siyassa da tattali tuttule tulun tulin dukiya.