Majigin kanen-Audu
Masana’antar sarrafa dodannin Majigin kanen-Audu ta shiga tsomumuwar mutanen gandun Gandi. Kuma idan har Jarumn juyin aya da su Zailla-ziyya da Zankada-ziyya suka yi sakaci,kowa sai ya iya faskaren ma’anonin “taimaki gatari, ka riki gatari,bi tara molaki ya ho!’ a cikin yaren Hau-hau wajen hawan sa ba tare da sa’in-sa ba. Don haka nike ganin […]
Masana’antar sarrafa dodannin Majigin kanen-Audu ta shiga tsomumuwar mutanen gandun Gandi. Kuma idan har Jarumn juyin aya da su Zailla-ziyya da Zankada-ziyya suka yi sakaci,kowa sai ya iya faskaren ma’anonin “taimaki gatari, ka riki gatari,bi tara molaki ya ho!’ a cikin yaren Hau-hau wajen hawan sa ba tare da sa’in-sa ba. Don haka nike ganin lokaci ya yi da masu laluben na-koko a wasannin majigin kanen-Audu su yi karatun wasikan jakin-dawa da na-gida a tsanake, ta yadda za su daina jefa azargagiyar zargin rushewar masana’antarsu; uwa-uwa su lalubo bakin zaren lilo don dinke baraka.
Ganin tsomomuwar da kanen Audu masu majigi suka shiga, shi yasa na ga ya kamata mu tallafa musu, musamman ma tunda GizBaba ya nuna gazawa wajen tsamo abokansa daga kulle-kuciyar da suke yi da mutanen Gandun- Gandi. Zabi dai ya rage muku, ko daii ku yi wa masana’antar Majigin kanen-Audu garambawul, ko kuma ku tsunduma cikin Bawalin-waga-dugu. Ganin muhimmancin da Haurobiyawa suka bai wa majigi, shi yasa mu ma za mu dan tabuka wajen yi wa wannan masana’anta sabon fasali, in ta kama ma mu yi mata manhaja, duk da cewa na san ba lallai ne su yarda, su daina hajijiya ba.
Batu na ingarman karafa, idan har masu laluben na koko a masana’antar Majigin kanen-Audu na neman tsira daga fallatsin Bawalin wasan-gudun Indiyawa, dole ne su yi yunkurin daukaka darajar al’adun masu magana da yaren Hau-hau wajen hawan sa ba tare da sa-in-sa ba. Domin yawan tsallen badaken da suke yi ne a cikin Bawalin-waga-dugu, ta sanya ake neman falle su su fadi kasa warwas.
Uwa-uba, akwai bukatar su Zilla-ziyya da Zankada-ziyya su daina wasannin zilliyya da zankade-zankade a dandalin majigi; su kuma kauce wa sharholiya da holewa. dabbaka irin wadannan dabi’u da muka zayyano su za su sanya nagarta a masana’antar majigin masu Magana da yaren hau-hau, har su yi ta hawa da sauka ba tare da sa-in-sa ba.
Idan har sun yarda za su dauki shawarar direban allli, to ina ganin abin da zai kara musu armashi shi ne, tunda yau Haurobiya ta cika shekaru babban lauje da tsayuwa bisa kafa daya da ’yancin walwala, amma tana fama da wahala, to sai ku lalubo yadda za a samu walwala.
Ganin cewa a cikin jiga-jigan masu wasan Samson-siya-siya da kwakwalen Haurobiyawa, akwai manyan taro ahu, to sai a yi kokarin saisaita kwanyar gama-garijn al’umma, don kada mu rika koyi da batagarin da suka hada da Akuyar-maman-daudu da gungun matasa da ke fafutikar dibar “TAN_TAN na dukiyar Haurobiya, wai don su agaza wa Shugaban Mai Gudun-loko ya Jona-tantin mulki, ko ana ha- maza, ha mata.
Bari dai in fito a cikin kankara ku ganni a fili, ko na nuna muku yadda za a shirya majigi a kan masu cako tsiyataku a kasar nan. Kowa ya san an wawurin Damin Dalar Hauron Amurkawa a tsuntsun saman Limamin Majami’ar Addu’a da gicciye na kasar Haurobiya, saboda haka sai mu nusar da hukuma cewa, ta tafka ta’asa a kwanon tasa, ko ta gyara ko ta shiga sa-in-sa da al’umma.
Masu wasannin majigi a rika fallen shafukan mujallu da jaridu, wadanda suka hada da Balon-faranti da Faffale dalili da Dalilin taronsu da Tarbar-bunu da Gadin-yana a Banga-da-gadi da makamantansu.
Lallai mu nemi Mai-duka ya yi mana katangar karfe da miyagun da ke cako tsiyataku su fake da tarzomar Haramta Bobo da kwambon Bokoko. Gudun lokon kuma ya isa haka nan. Sai mu hada karfi da karfe wajen yi wa tufkar hanci, ta yadda za a daina keta mana mutunci.
Sakon ’yan makaranta:
Muna murna Dodo
Assalamu alaikum bayan sallama irin ta masu kallon alkibla baki sili, a madadin daliban wannan makaranta tamu mai albarka, ta Dodorido da ke cikin shafin Amintattar jaridar da ake bugawa a Haurubja, babban birnin Haurobiya. Muna taya babban malamin wannan shafi da ma wasu shafukan jaridar Amintattar jarida, wato Malam Dodo da mai dakinsa samun karuwa da suka yi a makonnin da suka arce, na ‘yar dugwui-dugwu Nana Fadimatu Zaharau.
Yau kwanaki kofar hanci da babban lauje ke nan, Mai duka Ya yi mata albarka, Ya sa mahaddaciyar littafi mai girma ce, ya kuma ba mahaifiyarta koshinuwar jiki, ya kuma tunkudo wa malam Dodo da alheri baki sili. Duk wanda ya karanta, ya ce, amin.
DagaAliyu Mukhtar Sa’idu Jami’in hulda da jama’a na kasa 08034332200.
Batun kashin awaki ne ba kwai da dutse ba
Bayan sallama ta addinin masoyin da ba mu da tamkarsa(S.A.W), da jinjina ga daukacin ‘yan wannan makaranta tamu mai albarka da fadakarwa, ta Dodorido. Ina fatan daukakar masu daura dankwali da ma sauran al’umma baki sili za su fahimci abin da na bijiro da shi. Haba kashin awakina uwayen giji, ku gane ku fahimci cewa, tunkiyoyi kashin awaki ne, da ba ku, da sama das u, in kuka duba a zamantakewarku a karkashin inuwa sili, idan baki da koshin uwar jiki, kafin wata kashin awakinki ta sawo takwanta tinkis-tinkis ta iso, ita wannan ta kwibin taki, ta yi miki girkin kayan dundume kururu, tare da share damuwarki. Haka matsalarki ta haihuwa, da dawainiya ta cikin gida da kula da albarkatunki na manyan gobe, duk ta kwibin ki ce za ta yi hobbasa, kafin a ce wasu daga kashin awakin ki sun iso.
Kuma ku kwana tare, ku tashi tare, ga shi duk albarkatun manyan goben ku za su fito daga tsatso sili, wato bishiyar da kuke karkashinta kuna shan inuwarta. Don haka nike ganin ba matsala ba ce, don kun hada tumbi, sannan manyan gobenku za su samu yau da kullum din su goruba a hade, ba tare da nuna wa juna ‘yan bishiyanci ba, ko bayan ranku da bishiya za su rayu da son juna. Mai-duka ya sa iyayen giji su daina gajiyawa da guna-guni.
Daga karshe nike cewa fa kashin awaki ne ba kwai da dutse ba. Daga: A don gari Hafsat Jahar tumbin giwa 07032138614.