Majigin maganadisun masoyan Mekzikawa

Maganadisun masoyan Mekzikawa Matattarar masu kaiwa da komowa Masana’antar warwasawa da watayawa Hikayar holewa Tumbatsar tolatsewa   Karfa-karfan karafunan karfafawa Kundunbalar kadamusawan kundumewa Kwalam da makwalashen lamushewa Kwakwar kwacen kwakumewa Kadandoniyar kudundunewa   Rarrashin rangajin rausayawa Tangal-tangal din tokarewa Zugar zagayawa Zolayar  zababbakawa Zazzabin zogin zaman-tattakewa   Soyayya ce a kwanso Kowa ya samu kaso […]

Majigin maganadisun masoyan Mekzikawa

Maganadisun masoyan Mekzikawa

Matattarar masu kaiwa da komowa

Masana’antar warwasawa da watayawa

Hikayar holewa

Tumbatsar tolatsewa

 

Karfa-karfan karafunan karfafawa

Kundunbalar kadamusawan kundumewa

Kwalam da makwalashen lamushewa

Kwakwar kwacen kwakumewa

Kadandoniyar kudundunewa

 

Rarrashin rangajin rausayawa

Tangal-tangal din tokarewa

Zugar zagayawa

Zolayar  zababbakawa

Zazzabin zogin zaman-tattakewa

 

Soyayya ce a kwanso

Kowa ya samu kaso

Tunani ne ya taso

Son rai aka kwaso

Annakiyar adawa ke ta naso

 

Majigin mutsuttsukewa

Masana’antar maganin musgunawa

Damar karamin laujen kayatarwa

Soyewar zukata ba kakkautawa

Masoya na annurin annashuwa

 

An yi nunin nishadantarwa

Akwakwun hotunan Haurobiyawa

Masu wutsil-wutsil da wuntsilawa

Shirye-shiryen da ake shiryawa

Aika-aika ana dada aikatawa

 

Manhajar masoya

Maganadisun soyayya

Mirgina-mirginar sanayya

Mahangar kawar da kiyayya

Masalahar lumanar zuciya

 

Kannen-Audu

Kar ku bi inna rududu

Ku dafa ku hau tudu

Kui biyayya ga Gwaggo Dudu

Mutan Arewaci da na kudu

 

A bar handama da babakere

Lamarin da ke haifar da sare-sare

A zo ai ta faman gyare-gyare

Gudun kar kasa ta dare

Tuni masu gudu sun rare

 

Ka ga masu mare-mare

Za su zamto ’yan tabare

Lamura su tabarbare

Mu zamo babu bare

Har magabtanmu su sare

 

An ce ina batu da yare

Cewa nai rayuka a kare

Ba dawurwurin durwan kare

A kiyayi Harare-harare

Ballantana a kai ga hare-hare

 

Miyagu su yasar da al’umma su ketare

Dukiya duk sun tattare

Sun haddasa kalare

‘Yan jagaliya sun fandare

Barandami da gariyo an dire

 

A lura da masu raraka

Zagayowar zabuka

Ayyukan da suka tabuka

Ko sun yi aika-aika

Sai su sa ai ta kiki-kaka

 

Ga damar karamin lauje

Kar a bari komai ya baje

Managarta a ja mu je

Ban da wasan na jan je

Ai masalaha ciki da waje

 

Kisan gilla

Babbar kutungwila

Da ake yi wa juna illa

Talaka ya sha bulala

Da balbalin bala’in tsallen tsula

 

Dama ta sake zagayowa

A baiwa kowa-da-kowa

Ban da dira wawa

Ko asakalar hautsinewa

Wuta a yayyafa mata ruwa

 

Dunun dugunzumar damuwa

Danniyar hana damawa

Dundumin dulmiyawa

Dalilin durkushewa

Durfafar dambacewar dambarwa

 

Ai ta kokarin a gyara

A biya diyyar asara

Komai ai karara

Ban da kwado da dara

Sai al’umma ta sarara

 

Kira shagabannin kabila

Su zamto masu kula

A kiyayi kulla-kulla

Kar zarmewar lamura ta lula

A karke a kila-wa-kala

 

Bambamin bambance-bambance

Batancin batacce

Batan-baka-tantan

Buruntu da gangan

Baragurbi ya butulce

 

Batutuwa a tantance

Bilinbituwa a fayyace

Baragurbi ya susuce

Bayani a kai a kaikaice

Babban gari ya fi gaban kwatance

 

Ina malumma

A hada kai da hukuma

A nusar da mu alama

Sai kowa ya kama

Ai ta ba da himma

 

Ai kama-kama

Mu kara azama

Kasarmu ta kara kima

Tai dadin zama

Don tabbatar da salama

 

Wannan ita ce wasika

Kar a ce na rera waka

Hatsin tuwo a kyautata nika

Sana’ar na-duke sai a duka

A bar iska kowa ya shaka

 

Mai-duka ni na roka

Ya kwance mana sasarin sarka

Mugun zare kar ya zam na saka

Ai maganin kwashi-kwaraf da wadaka

A kawar da sara-sukar  wuka

 

Baban-burin-huriyya

Ka tarairayi Haurobiya

Rayuka a ba su kariya

A alkinta mana dukiya

Tallafin talaka ba shan wuya

 

Usainin-Babajo

Ka san aikin Baba-ojo

Shagaban masu gwanjo

Ya gwabje su gwarjo

Wajen taka rawar banjo

 

Gwamna el-Rusau

Ka zama Makasau

Jikan Kwasau

Magabta ka zame musu Korau

Batunka ba ai masa tasau

 

Mu ci dunun kiyayya

Dubi kasashen da su kai gogayya

’Yan siyasa na hamayya

Amma ba tsiya-tsiya

Kamun hannu ake kowa ya taya

 

Kundin kadan kudu

Kandamar kunu

Ko kamuwa da kurkunu

Kurda-kurdar hawan tudu

Karambani babu awon mudu

 

Arewatawa an shiga rudu

Tada kan adda ya yadu

Makirai sun harhadu

Badakalar baudaddu

Daukar alhaki ya sa an kwabdu