Majinyaci ya ki barin asibiti tsawon shekara uku a kasar Sin

Wani majiyaci dan kasar Sin ya ki barin asibiti har sai da ’yan sanda suka fitar da shi, bayan sun smau umarnin kotu. Wata kotu a birnin Beijing ta bayar da umarnin a fitar da mutumin dan shekara 55, wanda aka bayyana sunansa a matsayin Chen. Kuma ya shafe shekara uku yana kwance a asibitin. […]

Majinyaci ya ki barin asibiti tsawon shekara uku a kasar Sin
Majinyaci ya ki barin asibiti tsawon shekara uku a kasar Sin

Wani majiyaci dan kasar Sin ya ki barin asibiti har sai da ’yan sanda suka fitar da shi, bayan sun smau umarnin kotu. Wata kotu a birnin Beijing ta bayar da umarnin a fitar da mutumin dan shekara 55, wanda aka bayyana sunansa a matsayin Chen. Kuma ya shafe shekara uku yana kwance a asibitin.

An fitar da Mista Chen daga cikin asibitin Beijing Jingmei Group Hospital, bayan da aka umarce ya fice daga asibiti.
Mara lafiya ya daure kansa da ankwa a jikin gado, kuma ya yi ta kokowa da ’yan sanda har sai da suka fitar da shi daga asibitin.
Jami’an ’yan sandan da suka fitar da shi da karfi, sia da suka datse makullan da ya sanya ya daure kansa da ankwa, aka fito da shi sanye da rigar jinya, inda yake ta kokowa da jami’an tsaro.
An kwantar da Mista Chen a wannan asibiti ne cikin watan agustan shekarar 2011, inda aka yi masa maganin ciwon da ya yi fama da shi a sanadiyyar hadarin mota.