Majinyata na kuka da tsada da rashin kula a asibitocin koyarwa na Najeriya – Bincike
Binciken da jaridar Aminiya ta gudanar ya gano cewa tsofaffin kayayyakin aiki da lalatattun gine-gine da rashin samun isasshiyar wutar lantarki da kuma rashin isassun kudi su ne suke yi wa asibitocin koyarwa na Najeriya tarnaki tare da hana su gudanar da ayyuka ga majinyatan da suke fama da manyan cututtuka. Asibitocin sun kuma damu […]
Binciken da jaridar Aminiya ta gudanar ya gano cewa tsofaffin kayayyakin aiki da lalatattun gine-gine da rashin samun isasshiyar wutar lantarki da kuma rashin isassun kudi su ne suke yi wa asibitocin koyarwa na Najeriya tarnaki tare da hana su gudanar da ayyuka ga majinyatan da suke fama da manyan cututtuka.
Asibitocin sun kuma damu da yadda majinyata da dama suke tururuwa, inda hakan ke shafar aikinsu na ba da horo ga kwararrun ma’aikatan lafiya da ake da su a yanzu da kuma wadanda za a horar a nan gaba.
Kamar yadda wakilanmu suka ruwaito, majinyata na gumu wajen biyan makudan kudi da suka kamata su biya koda kuwa hakan zai dauki kwanaki kafin su samu ganin likita.
Sannan a lokuta da dama za ka iske dakunan gudanar da gwaje-gwaje da kayan aikin da ake bukata wajen yi wa masu fama da cutar daji da ta koda da kuma ta kwakwalwa da sauran manyan cututtuka aiki duk tsoffin yayi ne ko kuma lalatattu. Ko kuma a asibitocin za ka iya samun kayan aikin suna aiki amma fa babu wutar lantarkin da za a yi amfani da ita wajen aiki da su.
Binciken da wakilanmu suka gudanar, ya gano cincirindon majinyata da ake samu a asibitocin yana faruwa ne sakamakon yadda wadansu majinyatan suke fama da wasu cututtuka da za a iya magancewa a kanana ko matsakaitan asibitoci amma sai su wuce zuwa asibitocin koyarawar.
Haka kuma majinyatan sun koka game da rashin tsabta a cikin asibitocin, wanda hakn na iya sanya majinyata su kamu da wasu cututtuka na daban saboda rashin tsabtar magudanun ruwa da jibgin shara da budaddun makewayi da ake da su a harabobin asibitocin.

Majinyata na kwana a kan tabarmi a Asibitin Koyarwa na UDUTH, Sakkwato
Majinyata a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usman Dan Fodiyo da ke Sakkwato, wanda shi ne asibitin da yake karbar majinyata daga jihohin Sakkwato da Kebbi da Katsina da Zamfara da kuma wasu jihohi makwabta na kasar Nijar, suna kwana ne a kan tabarmi a sashen majinyata masu bukatar aikin gaggawa saboda rashin wadatar gadajen kwanciya. Alkaluman da ake da su sun nuna cewa a kullum kusan majiyanta 1000 ake sallama sannan a karbi dubu 17 da 133 wadanda duk za a iya magance lalurorinsu a kananan asibitoci.
“Wasu cututtukan ba wadanda za a zo mana da su ne a irin asibitocinmu ba. Cututtuka ne da za a iya maganinsu tun a kananan asibitoci. Kamata ya yi a ce muna nan cututtukan da suka yi tsanani ne za a kawo mana,” inji Malam Sani Abubakar, Shugaban Kungiyar Likitoci ta Kasa reshen Jihar Sakkwato.
A ta bakin wani ma’aikacin asibitin da ba ya son a fadi sunansa, cewa ya yi na’urar MRI wadda take da muhimmanci wajen duba cututtukan da suka shafi jijiyoyi, an dade da jingine ta, tun shekaru kamar 5 da suka wuce, sannan wasu na’urorin daukar hoton cikin jiki ba sa aiki. Sannan cikin na’urori 7 da ake da su na wankin koda, daya ce tal take aiki a halin yanzu.
Dokta Muhammad Makusidi wanda shi ne Shugaban Sashen Cututtukan Koda na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usman Dan Fodiyo, ya bayyana wa Aminiya cewa na’urori 6 sun samu matsalolin da suka hada da yin zafi sakamakon rashin isasshiyar wutar lantarki kuma wasunsu sun tashi daga aiki ne saboda tsufar da suka yi.
A Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abuja, rashin wadatar ma’aikata na barazana ga aikin duba marasa lafiya. Sannan ga wari ya addabi wasu sassan asibitin. Wakilinmu wanda ya kai ziyara asibitin, ya lura cewa a daya daga cikin dakunan kwanciya na maza da yake bangaren ‘ENT’ wari ne ya turnuke shi daga wata kwata da ke a bayansa. Sannan ya lura cewa wasu ramuka na masai kusan duk a bude suke.
Wata majinyaciya, Misis Jummai Audu ta ce a duk lokacin da za ta shiga wannan dakin sai ta yi amfani da mayani don toshe hancinta saboda doyi. Binciken da Aminiya ta gudanar, ya nuna cewa asibitin yana fama da karancin maa’ikata a bangaren dakunan gudanar da gwaje-gwajen kimiyya da bangaren magani da kuma bangaren ma’aikatan jinya.
Aiki na kwan-gaba-kwan-baya a Asibitin Koyarwa na Maiduguri
Kayan aiki da kuma yadda ake gudanar da aikin kansa a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri duk suna kwan-gaba-kwan-baya ne, wani lokaci a iske wani bangaren yana aiki wani kuma kuma ba ya yi. Wasu da yawa daga cikin na’urorin da ake amfani da su a asibitin kamar na’urar wankin koda duk tsofaffin yayi ne. Na’urorin wankin koda 2 ne kawai ke aiki a asibitin. Haka kuma na’urar daukar hoton surar halittar mutum guda daya ce a asibitin, wacce ita ma tana ba da tangarda a wasu lokuta, wanda hakan yake sa wa wasu lokuta tilas ake tura marasa lafiya zuwa Asibitin Kula da Tababbu na Maiduguri. A wasu bangarorin asibitin, ayyuka na gudana yadda ya kamata amma a wasu bangarorin kamar bangaren masu fama da ciwon zuciya, marasa lafiya sun yi wa likitocin da ake da su yawa.
A sashen ajiye gawa na asibitin ma, ayyukan ba sa gudana da kyau, babu kayan aiki isassu, ba ma kamar a ce idan an samu tashin bam da ke sanadiyyar mutuwar mutane da dama a kawo gawawwaki da yawa. A inda za ka ga yawan gawa ya wuce yawan na’urorin gidan sanyi da ake da su, wanda ala tilas za ka ga ana ajiye gawa waje a kan dabe.
A bangaren sashen fida kuma likitoci uku ne kawai ake da su duk da yake sashen yana bukatar fiye da haka. Shugaban Asibitin Farfesa Ahmed Ahidjo ya shaida wa Aminiya ta wayar tarho cewa asibitin ba ya samun isassun kudin da ya kamata, domin gabatar da ayyukansa cikin yanayi mai kyau.
Akwai matsaloli ta fuskar na’urori a Asibitin Koyarwa na Yola da Maiduguri
Wasu daga cikin majinyatan da Aminiya ta zanta da su sun bayyana cewa Naira dubu 15, da suke biya a duk wankin koda daya da aka yi musu sun fi karfinsu. Domin kuwa wadansunsu suna zuwa wankin sau biyu a cikin mako daya.
“Ya dauki mahaifina wata daya kafin a ba shi gado saboda karancinsa. Don haka akwai bukatar gwamnati ta kara gina wasu dakuna,” inji Sani Abadam.
Ya ce “Ayyukan gwajin jini da kuma daukar hoton cikin jiki ba su da wahala, duka ba su wuce minti 30, to amma za ka iske majinyata sun share awoyi suna kan layi, suna jira saboda yawan masu bukatar wadannan ayyuka.”
Wakilinmu ya ce a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri ba na’urar kankanta hoton surar sassan dan Adam (MRI) da na’urar daukar hoton kwarangwal (CT Scan) da kuma na’urar binciken ciwon daji (Cancer Screening Machine). Amma asibitin na da lafiyayyun na’urorin daukar hoton jiki da hadadden dakin gudanar da bincike da kuma lafiyayyun na’urorin wankin koda guda biyu.
Da aka tuntubi Jami’in Hulda da Jama’a na Asibitin, Adamu Dodo, cewa ya yi asibiti shi ne kadai irinsa a yankin, kuma saboda kayan aikinsa majinyata ke yin tururuwa daga Jihar Taraba, har ma daga wasu sassa na kasar Kamaru. Shi kuwa mai magana da yawun kungiyar likitoci ta Jihar Adamawa, Auwal Ibrahim cewa ya yi da dama daga cikin majinyata ba su iya biyan kudin da ake cajinsu.
Akwai matsalar gadajen kwanciya a Asibitin Malam Aminu Kano
A Asibitin Koyawar na Malam Aminu Kano kuwa, wakilinmu ya zanta da wadansu masu neman gado, inda suka bayyana masa irin wahalar da suke sha wajen neman gadon da za a kwantar da majinyatansu a matsayin babbar matsalar da take addabar masu jinya a asibitin.
Wani da aka kwantar da dansa a kan kunar wuta, Malam Musa Ibrahim ya ce dansa yana bukatar kulawar gaggawa saboda kunar da ke jikinsa amma sama da mako biyu ba su samu gadon kwanciya ba har sai da wani abokinsa ya sa baki kafin a kwantar da yaron dan shekara biyu.
Lokacin da wakilinmu ya ziyarci asibitin ya tarar da majinyata a karkashin bishiya tare da gidan sauro da tabarmi saboda rashin gadon da za su kwanta a kai.
Wani majinyaci da ke fama da cutar daji, Iliyasu Adamu ya ce ya shafe fiye da mako guda yana kwana a karkashin bishiya saboda bai samu gadon da za a kwantar da shi ba. Ya ce saboda nisa da yake da shi da matsin rayuwa da yake fama da ita, ya sa dole ya kwanta a farfajiyar asibitin kafin lokacin da za a yi masa aiki.
Wakilinmu ya yi kokarin zantawa da Shugaban Asibitin amma ya ci tura saboda an shaida masa cewa wai ya yi tafiya.
Akwai matsalar injin wankin koda Asibitin JUTH na Jos
Wakilinmu ya lura da cinkoson da ake yi a harabar karbar gwajin jini domin bincike. Wata marar lafiya, Fatima Ibrahim ta ce likitanta ya tura ta ta yi wasu gwaje-gwaje ciki har da gwajin dajin nono a matakin farko. Amma lokacin da ta je bangaren gwajin sai aka shaida mata cewa injin gwajin ya lalace sama da shekara guda da ta gabata.
“An tura ni zuwa wajen gwaji na masu zaman kansu shi ma dai na tarar injin yana da matsala sai kuma suka ba ni shawarar in tafi Asibitin Bukur. Sai dai har yanzu ban samu damar zuwa ba,” inji Fatima.
Wani da matarsa ke zuwa wankin koda, Kinsely Ekundayo ya ce duk mako yana kashe Naira dubu 60 kuma ya ce shekara guda ke nan suna wannan fama. Ya ce matsalar kodar matar tasa ta shafi wasu sassan jikinta kuma an tura su Kano domin wasu gwaje-gwaje saboda wannan asibitin ba ya da kayan aikin gwajin da za su yi.
Kinsely ya ce injin wankin kodar ba ya aikin da ya kamata, inda ya yi kira ga gwamnati ta sanya tallafi wajen kudaden da ake kashewa wajen wankin koda da sauran gwaje-gwajen da suke da tsada a asibitocin.
Abdulwahab Hassan da ya kamu da ciwon zuciya da hakan ya faru saboda matsalar cutar koda, matarsa Hussaina Hassan da take kula da shi, ta ce sun kashe makudan kudade wajen jinya.
Daraktan Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos, Dokta Anas Sabir ya zayyana wasu matsaloli da suke damunsu a asibitin.
“Wasu daga cikin injinanmu kamar injin daukar hoto na CT da injin kula da masu kansa da injin wankin koda, dukkansu ba sa aiki daidai. Hakazalika ba dukkan injinan da suke dakin tiyata ne suke aikin da ya kamata ba. Akwai wasu injinan da idan suka lalace muna gyara su domin a ci gaba da amfani da su,” inji shi.
Dokta Sani ya ce gurbin mutum 700 ne kadai a asibitin da ake kwantar da marasa lafiya a halin yanzu. Ya ce a matsayin asibitin na koyarwa, wannan adadin ya isa amma saboda yawan mutane da suke zuwa asibitin ya sa yake fuskantar matsaloli.
Shi ma Daraktan Asibitin Koyarwa da ke Uyo, Dokta Emembasi Bassey ya ce “Kafin in zama shugaban asibitin, ba mu da wutar lantarki sai daga baya muka sada asibitin da wutar lantarki. Kodayake har yanzu wutar ba ta samuwa sai dai mu yi amfani da injina domin samar da wutar da muke aiki da ita.”