Majinyatan harin bam a Kano sun samu tallafi
Gidauniyar tallafa wa wadanda hare-haren ta’addanci ke rutsawa da su ta ta ba da gudunmawar Naira miliyan 40 ga Asibitin koyarwa na Aminu Kano da kuma Asibitin Murtala, domin kulawa da mutanen da harin kunar bakin wake na kasuwar sayar da wayoyin hannu da ke Kano ya rutsa da su.Da yake mika gudunmowar, Babban Daraktan […]
Gidauniyar tallafa wa wadanda hare-haren ta’addanci ke rutsawa da su ta ta ba da gudunmawar Naira miliyan 40 ga Asibitin koyarwa na Aminu Kano da kuma Asibitin Murtala, domin kulawa da mutanen da harin kunar bakin wake na kasuwar sayar da wayoyin hannu da ke Kano ya rutsa da su.
Da yake mika gudunmowar, Babban Daraktan Gidauniyar, Farfesa Sunday Ochoche, wanda ya jagoranci tawagar jami’an gidauniyar, ya bayyana alhininsu dangane da harin da aka kai tare da jajenta wa wadanda suka jikkata da kuma yin ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasu sakamakon wannan hari.
Sannan ya sanar da cewa gidauniyar tasu ta ba kowane asibiti gudunmowar Naira miliyan 20, domin tallafa masu wajen kula da mutanen da harin ya shafa, tare da jaddada cewa an kafa gidauniyar ce domin ba da gudummawa ga wadanda harin ta’addanci ya rutsa da su.
A nasu bangaren, dukkan asibitocin sun bayyana cewa za su yi amfani da gudunmawar wajen kulawa da wadanda aka ba da tallafin domin su.