Majlisun jihohi sun zabi shugabanninsu

Majalisun dokoki na jihohi sun zabi sababbin shugabanninsu a ranar Talatar da ta gabata domin jan ragamarsu na shekara hudu masu zuwa. A Jihar Adamawa an zabi Kabiru Mijinyawa na APC daga Yola ta Kudu a matsayin shugaba da kuri’a 17 yayin da abokin takararsa Rufa’i Umar daga mazabar Gombi ya samu kuri’a 8, sai […]

Majlisun jihohi sun zabi shugabanninsu
Majlisun jihohi sun zabi shugabanninsu

Majalisun dokoki na jihohi sun zabi sababbin shugabanninsu a ranar Talatar da ta gabata domin jan ragamarsu na shekara hudu masu zuwa.

A Jihar Adamawa an zabi Kabiru Mijinyawa na APC daga Yola ta Kudu a matsayin shugaba da kuri’a 17 yayin da abokin takararsa Rufa’i Umar daga mazabar Gombi ya samu kuri’a 8, sai Sunday Peter ya zama Mataimakin Shugaban Majalisar ba tare da hamayya ba.
Sabon shugaban ya yi alkawarin warware takaddamar da ke tsakanin bangaren zartarwa da na majalisa da jihar ke fama da shi.
A jihar Kaduna Aminu Abdullahi Shagali ne sabon shugaban majalisar jihar, yayin da aka zabi Haruna M.A Inuwa a matsayin shugaban masu rinjaye sai Yusuf Ibrahim Zailani daga Igabi Babban mai tsawatarwa, sai Kantiok I. Ishaku daga Zankuwa shugaban marasa rinjaye.
A Jihar Neja wakilin mazabar Chanchaga a Jam’iyyar APC Abdullahi Marafa ne aka zaba a matsayin shugaban majalisar jihar ba tare da hammaya ba, sai kuma aka zabi Hussaini Ibrahim na APC daga Agaye a matsayin mataimakin shugaban majalisar ba hamayya.
A jawabinsa bayan zaben Marafa ya yi jama’ar jihar alkawarin gudanar da shugabanci nagari.
A Jihar Katsina ma an gudanar da zaben ne ta hanyar kada kuri’a tsakanin ’yan takara biyu da suka fito daga yankin Sanata na Daura, wato Alhaji Aliyu Sabi’u Muduru daga karamar Hukumar Mani da Alhaji Haruna Aliyu Yamel daga karamar Hukumar Dutsi, inda Aliyu Sabi’u Muduru ya yi nasara da kuri’a 28, Haruna Aliyu Yamel ya samu kuri’a 6.
Wannan ne karo na farko da wata jam’iyyar siyasa ta cinye zaben majalisar ba tare da ta samu abokiyar adawa ba.
Kuma an zabi Shehu dalhatu Tafoki daga karamar Hukumar Faskari a matsayin mataimakin shugaban majalisar bayan ya kada abokin takararsa Abdullahi Ibrahim Mahuta daga karamar Hukumar Malumfashi da kuri’u 26 da kuma 7.
Mambobin Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa sun zabi dan majalisar mazabar Ummaisha/Ugya Malam Ibrahim Balarabe na Jam’iyyar APC ne a matsayin shugaban majalisar, yayin da aka zabi wakilin Nasarawa-Eggon ta Kudu, Mista Godiya Akwashiki na Jam’iyyar PDP ya zama mataimakinsa, dukkansu an zabe su ne ba tare da hamayya ba.
Shugaban ya ce za su hada kai da bangaren zartarwa a jihar don tabbatar da sun kirkiro dokokin da za su inganta rayuwar al’ummar jihar. Sai ya bukaci takwarorinsa ’yan majalisar su ba su cikakken hadin kai don ta haka ne kawai za su cimma nasara.
A Jihar Filato Peter Azi na Jam’iyyar APC ne ya zama shugaban majalisar da Jam’iyyar PDP ke da wakilai 13 APC 11, bayan an kawo karshen tirka-tirka da ta taso yayin zaben shugaban majalisar wadda aka yi canjaras a karawar farko da kuri’a goma sha bibbiyu.
Peter Azi daga mazabar Jos ta Arewa maso Gabas ya zama shugaban majalisar ne, bayan da abokin takararsa tsohon shugaban majalisar Istifanus Mwansat na Jam’iyyar PDP daga mazabar Pankshin ta Kudu ya janye daga takarar. Kuma an zabi Adamu Gagdi (na PDP daga mazabar Kantana) a matsayin mataimakin shugaban majalisar.
A ranar Talata ne Gwamnan Jihar Filato, Simon Bako Lalong ya ba da umarnin dakatar da zaben saboda dalili na rashin tsaro kamar yadda Gwamnan ya ce a wata takarda da Akawun Majalisar ya karanta a gaban ’yan majalisar.