Makabartar Agege: Inda ake binne sabuwa da tsohuwar gawa a kabari daya
Ga dukkan alamu makabartar unguwar Markaz a yankin karamar Hukumar Agege da ke Jihar Legas, wacce al’ummar Nusulmi ’yan asalin Arewa da ke zaune a sassa da dama na jihar suka dogara da ita wajen binne mamatansu, ta shiga wani hali inda karancin wuri ya tilasta jama’a binne sabuwa da tsohuwar gawa a kabari daya. […]
Ga dukkan alamu makabartar unguwar Markaz a yankin karamar Hukumar Agege da ke Jihar Legas, wacce al’ummar Nusulmi ’yan asalin Arewa da ke zaune a sassa da dama na jihar suka dogara da ita wajen binne mamatansu, ta shiga wani hali inda karancin wuri ya tilasta jama’a binne sabuwa da tsohuwar gawa a kabari daya.
Shugaban ma’aikatan makabartar, Alhaji Babangida Haladu ya shaida wa Aminiya cewa karancin fili ne ya sa suke hada tsohuwa da sabuwar gawa a kabari daya.
Alhaji Babangida ya ce: “Gaskiya ne mukan hada tsohuwa da sabuwar gawa a kabari daya. Idan muka tona kabari don mu binne gawa mukan samu kai da sauran sassan jiki da kasusuwa na kafa ko na cinya, wani kabarin ma ba ma samun komai wani kuma sai mu samu likkafani babu komai a cikinsa duk naman mamacin ya bi kasa, saboda haka sai mu kwashe kasusuwan da muka samu na tsohuwa gawar sai mu kawo sabuwar gawar mu fara sakawa, mu sanya katako da kwalaye mu rufe ta, sannan sai mu kwaso kasusuwan tsohuwar gawar mu saka a cikin kabarin, sai mu binne su tare.”
Ya ci gaba da cewa: “Ba komai ba ne ya janyo haka, sai cika da makabartar ta yi. Saboda haka maimai muke yi. Idan muka kai karshe sai mu sake dawowa; haka muke yi shekara da shekaru. Kuma ina mai tabbatar maka da cewa wannan makabarta za ta ci gaba da daukar mutane ba tare da wata matsala ba. Shi ya sa nake bayar da shawara cewa ya kamata mu hakura da wannan makabarta mu ci gaba da binne mutanenmu a haka.”
Da yake jawabi, Hakimin Gabas kuma dan Iyan Agege, Alhaji danjuma Yakubu, ya bayyana cewa masarautar Agege tana yin iya kokarinta wajen ganin an samu maslaha dangane da batun makabarta a garin Agege.
Hakimi, wanda har ila yau yana daga cikin membobin kwamitin kungiyar Fauzil Azim da ke kan gaba wajen batun sayen sabuwar makabarta ya ci gaba da cewa: “Tuni aka riga aka sayi fili na sabuwar makabarta kuma wasu matasa sun fito sun fara aiki gadan-gadan don tabbatar da fara amfani da sabuwar makabarta, to amma sai aka samu tsaiko wadansu suka zo suka ce sune suka sayi filin.”
‘Suka ce sun sayi filin daga Lauya Yusuf. Shi kuwa Lauya Yusuf shi ya sayarwa da al’ummar Agege fili. Daga bisani da muka zurfafa bincike sai muka gano cewa tuni aka jinginar da filin ga wani banki saboda haka yanzu bankin shi yake da cikakken takardu na wannan wuri. Saboda haka daga bisani bayan fadar sarkin Hausawan Agege ta gano cewa bankin ne ke da ainihin takardun mallakar fili shi ne yanzu muke bi a hankali don mu samu mafita don kada ya zama mun fara binne jama’a a zo da katafila a tone su.” Inji shi.
Ya musanta zarge-zargen da wasu ke yi cewa masarautar Agege ce ke yin kafar ungulu da maganar makabartar.
“Ba gaskiya ba ne, duk wani aiki da zai zo in dai ta hanyar masarautar Agege ne muna da shaidu daki-daki. Ina mai ta==bbatar wa jama’a cewa tsaikon da aka samu ya zo sakamakon taka-tsan-tsan da muke yi wajen tabbatar da sahihancin abubuwa. Saboda haka ina kira ga jama’a su ci gaba yin hakuri su saurari masarauta nan gaba kadan za mu yi musu bayanai dalla-dalla.”
Da Aminiya ta tuntube Malami mai wa’azin Musulunci Ustaz Isma’il dalha Muhammad ya bayyana cewa matsala ce babba da ke tattare da tashin hankali.
“Gaskiya wannan babbar matsala ce kuma tana tayar mana da hankali saboda duk lokacin da ake binne gawa a makabartarmu sai ka ga an haka rami, ka ga ko dai a ciro gawa cikin likkafaninta ko a ciro kasusuwa ko ka ga likkafani ko wani abu makamancin haka, sannan a gyara kabarin sannan a saka wani. Ka ga wannan abu ba daidai ba ne to amma bisa lalura ake yi. Akwai ’yan uwa da suka kafa kungiya suka sanya mata suna Fauzil Azim, sun yin iya kokari su samar da sabuwar makabarta a Agege. Akwai wani fili da suka saya amma sai ya zama akwai matsala. Mun yi zama a gidan sarki amma har yanzu abubuwa ba su yanke ba, to amma har yanzu muna rokon Allah Ya kawo karshen wannan matsala’. Inji shi.