Makabartar da aka kai ni ce na ji ba ta yi min ba!

Wani mai sana’anta akwatin gawa ne aka kawo masa aikin yin akwatin ana bukatarsa da gaggawa, bayan ya gama ya sa a motarsa zai kai, yana cikin tafiya sai ta lalace. Sai ya yi shawarar dauka a kai ya karasa. Yana cikin tafiya sai ’yan sanda suka tare shi suka tambaya, “Ina zuwa?” Sai ya […]

Makabartar da aka kai ni ce na ji ba ta yi min ba!
Makabartar da aka kai ni ce na ji ba ta yi min ba!

Wani mai sana’anta akwatin gawa ne aka kawo masa aikin yin akwatin ana bukatarsa da gaggawa, bayan ya gama ya sa a motarsa zai kai, yana cikin tafiya sai ta lalace. Sai ya yi shawarar dauka a kai ya karasa. Yana cikin tafiya sai ’yan sanda suka tare shi suka tambaya, “Ina zuwa?” Sai ya ce “Wallahi makabartar da aka kai ni ce, na ji ba ta yi min ba, ina son in samu inda ba taro da yawa.” Sai ’yan sandan suka ruga a guje suka bar shi.
Hamza Yahaya