Makabartar Gombe da ake binne akalla jarirai 10 a kullum

Akalla jarirai 10 ake binne wa a kullum a Babbar Makabartar birnin Gombe da ke da nisan wasu ’yan kilomitoci daga cikin gari. Masu hakan kabari a makabartar wadanda suka tattauna da Aminiya sun ce a cikin wata uku, an binne gawarwaki sama da 750, ban da ma na jarirai. “Adadin bai ma kunshi na […]

Makabartar Gombe da ake binne akalla jarirai 10 a kullum

Sabbin kaburbura a Makabartar da ke Gombe

Akalla jarirai 10 ake binne wa a kullum a Babbar Makabartar birnin Gombe da ke da nisan wasu ’yan kilomitoci daga cikin gari.

Masu hakan kabari a makabartar wadanda suka tattauna da Aminiya sun ce a cikin wata uku, an binne gawarwaki sama da 750, ban da ma na jarirai.

“Adadin bai ma kunshi na wadanda ba a haifa da rai ba da kuma jariran da suka mutu kafin sunansu, su ba mu da bayanansu. Amma akalla, a kan binne jarirai 10 kullum a nan,” inji daya daga cikin masu hakan kabarin.

Mai hakan, mai suna Muhammadu Tasha mai kimanin shekara 57 a duniya ya kuma yi bayani kan yadda yake rayuwa da sana’ar ta hakan kabarin.

Ya ce kwata-kwata ba shi da wani lokacin walwala saboda ko da yaushe yana makabartar.

“Na kan yi aiki daga 7:00 na safe zuwa 8:00 na dare a duk ranakun mako saboda babu wani mai karbata.

“Bani da lokacin zuwa kowanne irin taron jama’a kamar daurin aure, radin suna ko gaisuwar mutuwa.

“Babban abin da ke debe min kewa shine iyalina. Bana jin haushin wannan aikin ko kadan saboda shine hanyar neman abincina.

“Al’umma kuma suna girmama ni matuka saboda ina yin abin da yawancinsu ba zasu iya ba,” inji shi.