Makabartun masu hali a Afirka
Daga Abubakar AbdurRahaman Dodo a Abuja da Ibrahim Abubakar a Legas da Isa Muhammad Inuwa a Kano Majalisar birnin Bulawuyo ta bude makabartar masu kudi, a wani wuri da ake kira Athlone West, inda ake biyan a kala Dala 500, wato daidai da Naira dubu 83, sannan bayan shekara biyar za a rika biyan rabin […]
Daga Abubakar AbdurRahaman Dodo a Abuja da Ibrahim Abubakar a Legas da Isa Muhammad Inuwa a Kano
Majalisar birnin Bulawuyo ta bude makabartar masu kudi, a wani wuri da ake kira Athlone West, inda ake biyan a kala Dala 500, wato daidai da Naira dubu 83, sannan bayan shekara biyar za a rika biyan rabin kudin, a matsayin haya, wato kashi hamsin cikin dari (Naira dubu 41da 500).
Majalisar mulkin wannan birnin ta yi hasashen samun akalla Dala miliyan hudu da dubu 700, inda aka samu nasarar sayar da kaburbura dubu takwas da 256.
Daraktar Kula da sashen Kula d alafiya, Zanele Hwalima, ta ce, sabanin sauran birane, Bulawayo bai taba samar da wata makabarta ta kasuwanci ba, alhali ofishinta na sane da cewa, akwai mkabartar ’yan kasuwa mai zaman kanta a Harare, babban birnin Zimbabwe.
Ta ce, wannan makabarta za a samar mata duk kayan da ak bukata, wadanda suka hada da wayoyin Katanga da kofar shia da fitilu, sannan za a tabbatar da tsaro.
Wakilanmu sun bi kadin yadda ake binne mamata a wadannan makabartu. Ga yadda al’amarin ya kasance:
Akwai makabartar masu kudi a Legas
A birrnin ikko akwai makabarta mallakar gwamnati, akwai kuma na masu zaman kansu, wadanda ’yan kasuwa ko kamfanoni ke da su, kuma kudi masu tarin yawa ne ake biya kafin a sayar don mallaki rami guda da za ka binne gawa ciki.
Akwai wadannan makabartun a wuraren da suka hada da Lekki da Ikoyi da Yaba, wadanda duka mallakar wasu mutane ne, kuma sun sayi filin ne daga hannun gwamnati, don haka ba wani haraji da suke biya, sai dai lokaci-lokaci akan bukaci su bayar da gudunmuwar su, wajen aikin gayya na unguwannin da makabartun suke, idan bukatar hakan ta taso.
Bambancin wadannan makabartun da na gwamnati, domin idan ka je na gwamnati, musammam a birnin Ikko, abu na farko da ke maka maraba da zuwa shi ne ciyawa, wani wurin ma ko da kudi aka hada ba za ka yarda ka shiga ba, kila wannan yasa ake da mutane a cikin su, koda yaushe, domin wanda ya zo neman binne gawa ya biya su kudi, su sare masa haki a inda aka bashi fili.
Shima na gwamnatin ana biya, amma ba abu ne da ya taka kara ya karya ba, sabanin na kudi, wanda yake a wadannan wuraren da ke da wadannan makabartan anan cikin birmin Ikko, ba inda yake kasa da Naira miliyan biyu, sai dai wajen tas-tas yake kai ka ce ba makabarta ba ce, sai domin cewa za ka ga gini irin na binne mutum, amma baya ga haka, akwai inda za ka iya sa tabarma ka kwanta hankalin ka kwance.
Misali makabartan EBONY da ke unguwar Yaba, a kan titin zuwa jami’ar Legas, ana sayar da rami daya na binne gawa a kan Naira miliyan biyu ne, kuma akwai na miliyan biyar, amma a bisa tsarin yadda ake binne mutane, shi ne kowane rami ana sa mutane uku ne, wato ana yi wa kowane rami matakali ko kuma hawa-hawa har ukku, suna kiran sa kabarin iyali.
Ana iya binne mutum guda, kana a bar filin mutane biyu da suke daga iyalin guda. Sai kuma wani lokaci idan wani ya mutu daga cikin wadannan iyalan sai a kara binne mutum guda, har sai sun kai su ukku; sai dai idan mutum daya ake so cikin rami guda, ana iya yin hakan, kuma tunda yake na sayarwa ne, ana sayarwa kowanne irin addini, ko musulmai ko kirista koma wadanda ba su da addini.
Su kuwa na Naira miliyan biyar, bambancin su da na miliyan biyu, shi ne, su suna cikin rumfa ne, ta yadda ruwa ba zai zuba kansu ba; kuma ba matacce ba, har ma mai rai na iya fake ruwa ko rana cikin wannan rumfar. Sannan a sauran makabartun, wato na bAULT GARDEN da ke Ikoyi, ana samun na Naira miliyan daya da rabi.
‘Akwai bangaren kwarori daban da na sauran mutane a makabartarmu’ – Wakilin Titin Katsina
A birnin Kano da kewaye an samu makabartar da ake binne kwarori ’yan asalin kasar Lebanon a gefe daya daban, sauran mutanen gari kuma musamman Hausawan da suka rasu ake binne su a daya gefen daban. Hakan kuma ya yi kama da makabartar Kabarin Raka da ke a unguwar Gama, ta yankin karamar Hukumar Nassarawa a yankin birnin Kano da kewaye.
Dagaci ko wakilin yankin Titin Katsina a Kano, kuma wanda makabartar sansanin alhazai ke karkashin yankinsa, Alhaji Sani Sambo kaura ya tabbatar wa Amniya cewa, tabbas da akwai bangaren kwarori daban da sauran bangaren mutanen gari a wannan makabartar.
“A sanina akalla wannan makabartar za ta kai shekara 100 da fara binne mutane a cikinta, kamar yanda na samu labarin daga mahaifina. Akwai bangare biyu, inda kwarori suke binne mutane da kuma inda sauran jama’a suke binne wa, amma kuma daga bisani kowa yana binne wa a kowane bangaren na makabartar,” inji shi.
Ya ce sai dai kwarorin sun fi binne wa a wannan bangaren da ake ganin nasu ne.
Ya musanta bayanin da wasu ke yi, cewa, ana bambanta tsakanin talakawa da masu kudi wajen binne gawa a makabartar, inda ya ce wannan maganar ba gaskiya ba ce, domin “kowa da kowa ya na binne wa da talakawa da masu kudi da malamai da kowa da kowa.”
Ya ce idan ma har da wani bambanci, bai wuce na tsakanin yanayin kaburburan kwarorin da na sauran jama’a ba.
A cewarsa: “Idan an haka kabarin ana mayar da kasar a rufe, wasu kuma suna bin gefen kabarin su gyara da sumunti ko marmara, amma su kwarorin kuwa za ka ga sun yi masa wani kyale-kyale kama da Tayil da kuma roduka na rila, su kewaye kabari.”
Ya ce akalla kwarorin sun kai shekaru 40 da fara binne mutanensu a wajen.
Ya ce gyara gefen da ake yi da marmara don kada ya baje ne, sannan kuma wadansu suna kafa alluna da rubutu game da mamaci a gefen kabarin, kamar yadda su ma kwarorin suke rubutu a jikin allon kabarin, inda ya ce makabartar tana da masu haka da masu kula da ita, kamar sauran makabartu; da masu kai ziyara, inda su ma kwarorin sukan kai ziyara, musamman a ranakun Alhamis da Juma’a.
“Ni dai a sanina ban san ana sayar da wajen ba, amma abin da na sani suna biyan mai haka, ya haka musu kabarin. Mutanenmu ma wani lokacin yakan ce a biya shi dubu biyu ko dubu daya”
Shi kuwa wani mai hakan kabari a makabartar mai suna Sharu Baita, wanda ya ce ya kai shekaru 45 yana aikin hakar kabari a makabartar, ya ce
A cewarsa: “Tarihin wannan makabarta, makabarta ce mai albarka wacce kowa yake son ya zo, kuma ana kawo manya-manyan mutanen da suka rasu a nan, kuma a kullum yini ake yi ana ziyara ta bayin Allah a nan.”
Ya ce daya bangaren na kwarori ne, kuma duk inda aka ga Tayil na kwarori ne, amma daya bangaren waje ne da ake binne manyan mutane da suka hada da Sheikh Tijjani ‘Yanmota da Sheikh Haruna Rashid Fagge da su Sheikh Manzo Arzai da Sheikh Malam Tijjani Zangon Barebari da sauran manyan malamai da Sharifai duk a nan aka binne su.
Da Aminiya ta so ta jin ko hakan ne ya sa ake ganin kamar ta manyan mutane ce, sai ya ce ko kadan ba haka ba ne. Ya kara da cewa dalilin da ya sa kwarori ke binne mutanensu a wajen shi ne, saboda su suka tambayi izini daga Marigayi Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na I, kuma aka ba su izini su rinka binne wa a wajen.
Da Aminiya ta tambaye shi adon da ake yi wa kaburburan, sai ya ce “a’a ni iyakacina haka ne nawa, amma su suke kawo masu gininsu da komai da komai a yi musu kuma duk wanda ya ce ana sayar da wajen binne mutane a nan karya yake yi.”
Ya ce, sai dai idan ya haka kabarin akan kawo abin sadaka a ba shi, wannan shi ne kawai abin da ya sani. Ya kuma ce yana bukatar gwamnati ta taimaka musu a bisa gudummawar da suke bayarwa ta sadaukar da rayuwarsu wajen hakan kabari.