Makada da mawaka mu guji yin hassada ga junanmu – Yahaya Sabuwar kasa
Alhaji Yahaya ’Yan Biyu da ke zaune a garin Sabuwar kasa da ke karamar Hukumar kafur da ke Jihar Katsina. Makadin kotso ne da ya yi fice wajen yi wa sarakunan gargajiya da ’yan siyasa wakoki a Arewacin Najeriya. A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu, ya bayyana yadda ya fara wannan sana’a ta […]
Alhaji Yahaya ’Yan Biyu da ke zaune a garin Sabuwar kasa da ke karamar Hukumar kafur da ke Jihar Katsina. Makadin kotso ne da ya yi fice wajen yi wa sarakunan gargajiya da ’yan siyasa wakoki a Arewacin Najeriya. A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu, ya bayyana yadda ya fara wannan sana’a ta kida da waka da kuma irin nasarorin da ya samu a sana’ar. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
Da farko sai ka fara da tarihin rayuwarka.
To, ni dai sunana Alhaji Yahaya ’Yan Biyu Sabuwar
kasa, makadan kotso da ke karamar Hukumar kafur a Jihar Katsina. Kakana Umaru Mai Kotso, makadin Sarkin Katsina Dikko ne kuma shi ne ya kawo shi garin Malumfashi. Haka kuma babana Alhaji ’Yan Biyu Sabuwar kasa, shi ma makadin Galadiman Katsina ne.
Yaya aka yi ka shiga wannan sana’a ta kidan kotso?
A gaskiya da ba wannan sana’a ta kida ne a gabana ba, duk da cewa na gaji wannan sana’a a wajen kakana da mahaifina. A da ina sana’ar noma da kasuwanci ne amma idan aka ce za a tafi kidan nan, nakan dauko kotsona na bi mahaifina don na sami gamawa lafiya. Sai kanina Alhaji Audu ’Yan Biyu ya rungumi wannan sana’a yana bin mahaifinmu, har ya yi fice. Sai aka rika kiransa muna tafiya ko’ina, mu je mu dawo lafiya. Sai Allah Ya yi wa wannan kani nawa gajeren kwana, daga nan sai na rungumi wannan sana’a na rika bin mahaifinmu. Da mahaifinmu ya ga haka sai ya ce mani ga yaransa nan, na rungumi wannan sana’a na rike kowa, ga amana nan zan ga amfaninta. Yau ina da shekara 19 ke nan da fara wannan sana’a.
Daga lokacin da ka fara wannan sana’a zuwa yanzu, wadanne irin nasarori ne kake ganin ka samu?
Na sami nasarori masu tarin yawa a wannan sana’a. Nasara ta farko da na fara samu ita ce, a lokacin marigayi Shugaban kasa Alhaji Umaru Musa ’Yar-aduwa yana Gwamnan Jihar Katsina. Aka shirya wani biki a garin Katsina, a wannan biki an ba ni motoci guda biyar. Bayan haka, an ba ni kujerar Hajji na je, an ba ni na kai ’yan uwa
da dama zuwa aikin Hajji. Bayan haka, ta dalilin wannan sana’a na kara gona kuma dukkan mutanen da mahaifina ya bar ni da su, kowa ya yi muhalli.
Kamar wadanne wurare ne ka je don gudanar da wannan sana’a?
Na je wurare da dama a Najeriya har kasar Nijar don gudanar da wannan sana’a.
Mene ne babban burinka a wannan sana’a?
Babban burina shi ne na ga cewa na gama lafiya a kan wannan sana’a.
Mene ne sakonka ga masu wannan sana’a?
Sakona ga dukkan masu wannan sana’a ta waka shi ne, kada su tsaya a kan wannan sana’a ita kadai. Kowa ya samu ya kara wata sana’ar. Kuma ina kira ga maroka kan mu guji yin hassada ga junanmu.