Makafi sun nuna rashin jin dadinsu ga Gwamnatin Adamawa
A kalla makafi sama da dubu daya ne suka hadu da fushin ’yan sandan da ke gadin babbar kofar Gidan Gwamnatin Jihar Adamawa lokacin da suka gudanar da zanga-zanga kan rashin damawa da su da Gwamnatin Bindow Jibrilla ba ta yi. Makafin sun yi korafin cewa ’yan sandan sun walakanta su sannan suka ce da […]

A kalla makafi sama da dubu daya ne suka hadu da fushin ’yan sandan da ke gadin babbar kofar Gidan Gwamnatin Jihar Adamawa lokacin da suka gudanar da zanga-zanga kan rashin damawa da su da Gwamnatin Bindow Jibrilla ba ta yi.
Makafin sun yi korafin cewa ’yan sandan sun walakanta su sannan suka ce da yawa daga cikinsu sun lallasa su a ofishin ’yan sandan, inda suka ce hakan bai dace ba, domin sun zo neman hakkinsu ne.
Shugaban kungiyar Makafi ta Jihar Adamawa, Mista Tizhe Kwada ya bayyana hakan ne ga manema labarai lokacin da rikici ya barke tsakaninsu da ’yan sandan a kofar gidan gwamnatin jihar.
Tizzhe ya ce sun je ne don nemi izinin shiga gidan gwamnatin domin kai kokensu bisa ga alkawuran da gwamnatin ta yi musu wadanda ba ta cika ba, dalilin ke nan da ya sanya suka shirya zangar-zangar lumana don nemi ganawa da Gwamnan Jihar amma ba a ba su damar yin hakan ba.
Shugaban makafin ya ce “Gwamnati ta hana mu bara, sannan babu wani aiki da ta ba mu ko ta koya mana domin ciyar da iyalanmu, sannan jami’an tsaro na korar mu idan mun fito bara ya yi yawa ainun.”
Tizhe ya kara da cewa dukan wulakanci ko korar da ’yan sandan za su yi musu da cin mutunci sai dai su yi, amma hakan ba zai sa su canja ra’ayinsu na ci gaba da gudanar da zanga-zangar ba.
Daga bisani Kwamishinan Harkokin Mata da Walwalar Jama’a, Usman Tola ya saurari korafin nasu tare kuma da yi musu alkawarin cewa zai yi iyakar kokarinsa don ganin cewa gwamnatin ta duba lamarin nasu sannan ya ba su hakuri bisa wulakancin da suka ce ’yan sanda sun yi masu.