Makafi ‘Yan Uwa uku Masu Sana’ar Nikan Albo sun nemi taimakon jama’a
Wasu magidanta uku ‘yan uwan juna da Allah ya jarabta da lalurar makanta suka kuma riki sana’ar nika garin albo domin dogaro da kai sun bukaci jama’a su kawo masu dauki duba da tsufan injin nikan nasu wanda suka kwashe sama da shekaru 30 suna amfani da shi. A shekarun baya Aminiya ta kawo labarin […]
Wasu magidanta uku ‘yan uwan juna da Allah ya jarabta da lalurar makanta suka kuma riki sana’ar nika garin albo domin dogaro da kai sun bukaci jama’a su kawo masu dauki duba da tsufan injin nikan nasu wanda suka kwashe sama da shekaru 30 suna amfani da shi.
A shekarun baya Aminiya ta kawo labarin magidantan da ke zaune a garin Agbo Aare da ke yankin Ogun ta Gabas da ke daura da garin Shaki a jihar Oyo.
Magidantan da suke ‘yaya ne ga tsohon limamin garin Agbo Aare wadanda lalurar makanta ta same su daya bayan dayan a lokacin da suke cika shekaru 30 a duniya.
Wakilin Aminiya ya ziyarci magidantan inda ya iske suna gudanar da rayuwarsu ta hanyar sana’ar da suke dogaro da ita na nikan garin also wanda suke yi da injin lista, injin da daya daga cikin su ya saya tun gabanin larurar makantar ta same su, sama da shekaru 30 da suka gabata.
Muhammadu Sa’adu Isiyaka wanda shine mafi yawan shekaru a tsakanin magidantan uku, mai kimanin shekaru 60, ya shaida wa Aminiya cewa ya wayi gari ne ya sami kan shi cikin makanta a lokacin yana da kimanin shekaru 30, yace yadda makantar ta same shi haka ta kama ‘yan uwansa maza biyu wadanda suke uwa daya uba daya, yace kafin larurar makantar yana aikin gyaran radiyo ne a jihar Legas amma tun lokacin da ya wayi gari da lalurar sai aikin gyaran radiyon ya gagare shi.
“Ko da na dawo gida daman kanina mai biye min mai suna Sulaiman Isiyaka ya sayi injin nika garin albo, ya bayar ana yi masa aiki, sai na shiga cikin masu aikin da ikon Allah cikin kankanin lokaci na lakanci yadda ake aikin, shima karamin cikin mu mai suna Nasiru Isiyaka da lalurar makantar ta same shi, sai yazo muka kama aikin nikan garin albon, yanzu mu biyu ne ke yin wannan sana’ar, shi kuma dayan kanin nawa yana yin kasuwancin tumaki da awaki ne a kasuwar dabbobi ta garin Agbo-Aare.
“Tun da wannan lalura ta same mu sama da shekaru 30 bamu taba yin bara ba, domin bara kaskanci ne da kashe zuciya, mu kuma jinin sarauta ne, inka lura zaka ga fuskokinmu da tsage, irin wannan tsage na saraki ne da ke mulkin jihar Oyo, in ka kula irin tsagen da ke fuskar babban basaraken jihar Oyo ke nan wato Alafin na Oyo, dan haka mu ba za muyi bara ba, don bai kamata ace ga jinin saraki na yin bara ba”, inji shi.
Yace babban kalubalen da suke fuskanta shine inji da suke amfani da shi wajen sana’ar tasu ya tsufa ya zama tsohon yayi ta yadda gyaran shi yake basu wahala, yace sun nemi taimako wajen gwamnatin jihar Oyo, ba sau xaya ba ba sau biyu ba, amma sun gaza samun tallafi.
“Ko a baya bayan nan mun rubu wa gwamnatin jihar Oyo takardar neman taimako amma har yanzu babu wani tallafi da muka samu, ga duk alamu gwamnatin tayi mana nisa ne, don haka muka ga ya dace mu nemi taimako wajen al’ummar Annabi, idan da mai hali da niyya ya taimake mu ya sai mana injin niqa na zamani wanda ke da saukin gyara” inji shi.
Ya kara da cewa baya ga sana’ar niqan garin albo za su iya yin sana’ar sayar da sassan injin nika, domin dadewarsu a sana’ar ta sanya shi kwarewa a sanin sassan injin nika, “idan na sami jari zan iya fara sayar da sassan injin nikan, don haka muna kira ga daidaikun jama’a da ita kanta gwamnatin da ta tallafa mana, ta yadda za mu cigaba da dogaro da kanmu akan sana’ar da muka rike” inji shi.
Fatan ‘yan uwan juna su uku masu lalurar malanta shine samun tallafi domin cigaba da gudanar da sana’arsu wacce suke dogaro akan ta wajen sauke allurar su da ta iyalansu.