Makafi za su mamaye Abuja – Sarkin Makafi

Makafi sun shirya gangamin mamaye Abuja don nuna takaicinsu kan yadda wani jami’in hukuma ya ziyarce su, ya kuma yaudare su ta hanyar yi musu alkawuran da suka hada da gina musu gidaje da ba su jarin Naira dubu 500, amma a karshe aka kare ba tare da samun ko daya ba, kamar yadda Sarkin […]

Makafi za su mamaye Abuja – Sarkin Makafi

Makafi sun shirya gangamin mamaye Abuja don nuna takaicinsu kan yadda wani jami’in hukuma ya ziyarce su, ya kuma yaudare su ta hanyar yi musu alkawuran da suka hada da gina musu gidaje da ba su jarin Naira dubu 500, amma a karshe aka kare ba tare da samun ko daya ba, kamar yadda Sarkin Makafin  Garki ya bayyana wa Aminiya.
A ziyarar da Sarkin Makafin Garki Abuja, Alhaji Abubakar Umar ya kawo ofishin Aminiya, tare da rakiyar Sakataren kungiyar Makafi ta Arewacin Najeriya, Malam Suleman Muhammad, ya bayyana hakikanin abin da ya auku tsakaninsu da Alhaji Iliyasu O. AbdurRa’uf, wani jami’in a ofishin kula da ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, sashen tallafa wa nakasassu, wanda ya je har gidansa, suka kuma rankaya zuwa gidan Sarkin Garki, wato Ona, don kafa hujja.
“Duk abin da zan yi sai na hada da Sarki Ona na Garki, don haka da ya zo ya ce zai gina mana gidaje, ya rushe bacocinmu da ke Karmajiji, sai muka tafi gaban sarki. Sarki ya nuna masa cewa wannan fili na wani ne, amma ya nuna cewa ya tunubi masu filin,” inji shi.
A cewar Sarkin Makafi, Alhaji AbdurRa’uf, ya zo ya fara gina wani gida, wanda ya ce na Sarkin Makafi ne, amma muka ce kada ya jawo mana rikici, don haka muka ba shi shawarar lallai ya mayar da wannan gini dakin shan magani ko asibitin nakasassu, inda gurgu da makaho da kuturu duk za a rika kula da lafiyarsu. “Zancen da nike yi maka har yau ba a ci gaba da wannan gini ba,” inji shi.
Sarkin Makafi ya ce daga bisani wannan mutum ya dawo ya ce ya samu wani fili, domin Shugaban kasa ya turo shi, ya yi yaki da fatara da talauci a tsakanin nakasassun da ke jihohi 19 na kasar nan. Kuma daga nan ya umarce mu mu tara makafi, a ranar biyu ga watan azumin Ramadan, muka kuma cika takardu neman tallafi. Daga nan sai ya zo da ma’aikatan bankunan Zenith da UBA ya rika daga cekin kudi mai dauke da Naira dubu 500, inda ya ce zai sallami kowa a wannan ranar, a cewarsa. Da muka nuna shakku, sai ya yi dabarar da ya yi ya bace, har yau bai sake dawowa ba.
Ya ce, a wannan taron makafi da aka sanya mu muka shirya, duk sai da na karar da abincin gidana, na kuma nemi kudin da zan sallami wadanda muka gayyato, kuma a karshe wannan al’amari ya zame mana masifa, domin ’yan fashi sun tare mutanenmu, inda suka tambaye su kan lallai su kawo kudin da suka ‘karbo a Abuja.’
“Bayan mutmin nan ya jefa mu cikin wahala da masifa, sai kawai muka ji labari wai ya fito a kafafen yada labarai, yana cewa ya raba mana jarin Naira dubu 500. karin abin haushi ma sai aka gano mana shi a wata jaridar Turanci mai taken National Trail, yana bayanin miliyoyin kudin da aka kawo na tallafa wa nakasassu, al’amarin da ya ce zai fara gudana ranar 15 ga Agusta, amma har yanzu ba mu ga komai ba,” inji shi.
Babban Sakataren kungiyar Makafin Arewa ta Northern Blind Unity Forum, ya ce matakin da muka dauka shi ne, mun aike da takardun korafi ga hukumomin da abin ya shafa, wadanda suka hada da Ma’aikatar Mata da kyautata walwalar al’umma da Hukumar Kula da Babban Birnin Tarayya da Sashen Kula da Tallafa wa Nakasassu na Ofishin Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya da Hukumar Tsaftaccen Muhalli ta Birnin Tarayya, kan lallai su warware matsalar da ke tsakaninmu da Illyasu O. AbdurRa’uf ko kuma nan da ranar 29 ga Oktoba za mu kira gagarumin taron makafi su mamaye Abuja. “Za mu yi zaman dirshan har sai an biya mana bukatarmu ko kuma a kasha mu,” inji shi.
Sarkin Makafi da Babban Sakataren kungiyarsu, sun karkare bayanansu da cewa wannan manufa tasu ta mamaye birnin Abuja, tare da tara makafi su yi zaman dirshan ba ta saba wa tanade-tanaden dokokin da ke zayyane a Kundin tsarin mulkin kasar nan ba. “Don haka a biya mana bukatunmu, a kwato mana hakkinmu, a matsayinmu na ’yan kasa, ko kuma abin da muka kuduri aniyar aiwatarwa, babu gudu, babu ja da baya,” a cewarsu.
Wadannan wakilai na makafi sun bai wa wakilin Aminiya daukacin kofen takardun da suka aike wa hukumomi da ma’aikatun Gwamnatin Tarayya, wadanda ke dauke da korafinsu game da wannan mutumin da ya wakilci shugabansa, har ma suka kara da cewa ya yaudare su da addini. “Ga ma takardar da ke dauke da sunan kungiyarsa ta Musulunci, Jam’iyyat Lutfillahi.” Takardar na dauke da makala kan yaki da fatara da talauci, bisa tsarin addinin addinin Musulunci, wadda wani masani mai digiri na biyu daga Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, mai suyna Salimonu Monsuru ya gabatar.
Aminiya ta tuntubi wanda makafin suke zargi Alhaji Ilyasu Olaruwaju Abdurra’uf wanda ya bayyana cewa, barazanar da makafi suka yi na shirya gangami a kan zargin yaudara da suke zargin ofishinsa da yi musu ba zai sa su watsar da sharadin da suka gindaya musu na kafa kungiya ba. “Illa iyaka za mu sanar da hukumar tsaro aniyarsu don daukar mataki da ya dace.’’    
Ya ci gaba da cewa, “aikinmu shi ne tabbatar da walwalar nakasassu a kasar nan. ta hanyar dora su a kan turbar sana’a da za mu ba su horo a kai, bayan sun zabi wanda suke so, kamar kiwon kifi ko kaji ko dabbobi da dai sauransau, mun kuma dauki jagora a kan wannan fuska don bada horo a cibiyoyi da za mu gina. A game da nakasassu da suka yi korafi a kanmu kuwa, mun bukace su da su kafa kungiyoyin sana’a, kamar yadda ka’idarmu take, a matsayin sharadi, wanda ba zai gaza ta mutane goma ba da za su yi rajista da mu tare da bude asusun ajiya a bankin UBA, za su rika hulda da su a madadinmu a ta bangaren kudi.’’
‘’Yanzu haka muna gina cibiyar ba da horo a garin Karma-jiji da kuma rukunin gidaje na nakasassu da za mu gina don sama musu mahalli. Za mu yi amfani da kudi ne da muka ware Naira dubu 500 ga ko wace karamar hukumar Abuja, a cikin guda shida da ake da su. Daga cikin kudin tallafi da muka samu daga cibiyoyi da ke da nasaba da gwamnati, kamar bankin raya noma da kuma Nedim Bank. A yanzu haka tuni gwamnatocin jihohi 9 suka nuna sha’awarsu tare da ba mu fili don gina cibiyoyinmu a yankunansu.’’