Makafin Dala: Garin naƙasassu da kowa ke ta kansa
Ya kamata su bar harkar bara kwata-kwata, su samu wata sana’a su riƙa yi.
Makafin Dala kamar yadda sunan ya nuna wuri ne da masu lalurar gani suke zaune a Jihar Kano.
Duk da cewa a yanzu unguwar ta cika da masu lafiyar idanu, sai dai har yanzu akwai makafi a unguwar da yawansu ya haura 300 kamar yadda Sarkin Makafin Kano ya shaida wa Aminiya.
Duk wanda ya san yankin Dala a Kano zai fahimci cewa makafin da ke yawon bara a unguwannin Gwammaja da Kantudu da Kurna da Ƙoƙi da Kofar Mazugal da Jakara daga Makafin Dala suka fito.
Abin da mutane ba su sani ba, shi ne baya ga bara waɗannan mutane sun iya sana’o’in hannu da suka haɗa da saƙa da aikin kafinta da sauransu.
Sai dai waɗannan mutane sun koka game da yadda duk da cewa sun samu horo a sana’o’in hannu, amma an yi watsi da su saboda an bar su kara-zube kuma gwamnati ta yi watsi da su ya sa ba su da wani zaɓi da ya rage illa su riƙe bara hannu bibbiyu.
- Nan da mako huɗu Nijeriya za ta daina sayo man fetur daga waje — Dangote
- Babu mulki mafi muni a tarihin Nijeriya kamar na Buhari — SDP
Malam Ado Halilu Abdulkarim shi ne Sarkin Makafin Kano ya jingina tarihin Makafin Dala zuwa zamanin Sarkin Kano Abdullahi Bayero wanda ya yi ƙoƙarin haɗa makafin Kano a wuri ɗaya inda ya ajiye su a Dala.
Ya ce, “A wancan lokaci Sarkin Kano Abdullahi Bayero ya yi ƙoƙarin harhaɗo makafin da ke wurare daban- daban a Masarautar Kano, misali waɗanda suke Bichi da Ɗambatta da sauransu, inda ya haɗe su a wuri guda wato a yankin Dala.
Kasancewar Malam Abdulkarim yana da ilimi sai aka sa ya zama shugabansu. Sai ya sa musu lokaci yana koyar da su littattafan Addinin Musulunci.
Za su je bararsu sannan idan sun dawo su je su ɗauki karatu a wajensa.”
A cewar Sarkin Makafin Kanon, a wancan lokaci makafin ba su yin kowace irin sana’a sai bara har zuwa lokacin da gwamnati ta yi tunanin canza wannan al’ada inda ta tura su don su samu horo a kan sana’o’in hannu daban-daban.
Ya ce yana ɗaya daga cikin mutanen da aka tura da farko zuwa Legas da Enugu don koyo sana’o’i. “Bayan mun dawo kuma muka ci gaba da koya wa sauran ’yan uwanmu abin da muka koyo.
Ina iya tunawa a wancan lokaci ina yin gadon jarirai na gargajiya da tabarmi da sauran abubuwa daban-daban.
A haƙiƙanin gaskiya mun amfana daga wannan sana’a inda mutanenmu da dama suka daina bara, suka mayar da hankali wajen yin sana’o’i daban-daban,” in ji shi.
A cewar Sarkin Makafin a yanzu haka mafi yawan masu jagora ga makafin da ke unguwar suna zuwa makaranta, “Mafi yawa daga cikin ’yan jagoranmu sun zuwa makaranta, muna ɗaukar nauyinsu.
Duk da cewa ba mu yi karatu ba mun gane cewa ilimi yana da mafani. Don haka idan muka je bara tare da su da safe, to, da yamma kuma za su tafi makaranta,” in ji shi.
Muhammad Inuwa Naira Dubu, ya bayyana wa Aminiya cewa yana ɗaya daga cikin waɗanda aka ba horo a kan sana’ar saƙa a wancan lokaci.
Sai dai daga baya da aka rufe cibiyar koyon sana’o’in da ke Mariri aka sallame su daga aikin shi ke nan ya zama ba ya da makoma sai dai ya koma ya ɗauki ƙoƙon bararsa.
“Zan iya tunawa a lokacin mulkin Gwamnan Jihar Kano Abubakar Rimi gwamnati ta raba mu da yawo a titi inda ta koya mana sana’a. Ni an koya min saƙa.
“Bisa taimakon Allah a wancan lokaci mutane suna sayen kayayyakin da muke saƙawa. Ba mu san dalilin da ya sa gwamnati ta sallame mu sannan ta rufe wurin ba.
“Tun daga wancan lokaci kuwa ungulu ta koma gidanta na tsamiya muka ci gaba da bararmu,’’ in ji shi.
Ya koka kan yadda gwamnati ba ta kula da buƙatunsu kamar yadda ta yi a baya.
“Lokacin da aka buɗe wannan cibiya tamu, Gwamnatin Rimi ta riƙa ba mu alawus duk wata sannan ta ɗauki wasu nauyinmu, sai dai wannan abu ya tsaya tun da daɗewa.
“Mafi yawanmu muna yin bara ce saboda gwamnati ta yi biris da mu. Da a ce gwamnati za ta waiwaye mu ta sama mana abin yi, na yi imani tunda ina daƙwarewar sana’ar da na koya, to da na yi sallama da bara,” in ji shi.
A cewar Inuwa Naira Dubu, mutum ya fi jin daɗi idan ya kasance shi yake bayarwa ba kullum ya riƙa miƙa hannu yana karɓa ba.
Ya ce, “Abu ne mai kyau a ce mutum shi yake bayarwa ba koyaushe ya zama yana miƙa hannu ana ba shi ba.
“Na fi so in yi aiki in samu kuɗi, maimakon inayi bara.”
Al’ummar sun nemi gwamnati ta yi dubi ga matsalolinsu ta hanyar mayar da su bisa tsarin karɓar alawus wata-wata sannan akwai buƙatar gwamnati ta tsaya musu wajen samun ilimi domin ƙarfafa wa makafin gwiwa su nemi ilimi don dogaro da kansu.
Malam Ibrahim Abdu ya koka game da yadda a matsayinsa na makaho a ce shi yake ɗaukar nauyin karatun ’ya’ya takwas ba tare da taimakon gwamnati ba.
“A matsayina na mai lalurar gani ni nake ɗaukar nauyin karatun ’ya’yana takwas.
“Akwai waɗanda nake biya musu Naira dubu 20, wasu dubu 40 kai har da wanda nake biya wa Naira dubu 50,” in ji shi.
Jamilu Isyaku makaho ne wanda yake fafutika a kullum don samun abin da zai sa a bakin salati ta hanyar bara, ya ce babban burinsa na son zama masanin kimiyyar siyasa ya haɗu da tasgaro sakamakon rashin samun wanda zai ɗauki nauyin karatunsa.
Ya ce ya zama tilas a gare shi ya bar makaranta ya fara bara saboda gwamnati ta gaza ɗaukar nauyin karatunsa.
“Na gama karatun sakandare a Makarantar Naƙasassu da ke Tudun Maliki.
“Na so in zurfafa karatuna, sai dai hakan bai yiwu ba, saboda tsufa ya cimma wa mahaifina ga matsin tattalin arziki da ake fama da shi hakan ya janyo ya kasa ci gaba da ɗaukar nauyin karatuna, don haka na fara bara.
“Abin da ciwo a ce tun shekarar 2020 da na kamala sakandare har yanzu na kasa ci gaba da karatu.
“Ko a yanzu idan zan samu wanda zai ɗauki nauyin karatuna zan bar bara in koma makaranta don ni ma rayuwata ta inganta,” in ji shi.
Da yake ƙarin haske game da irin halin da makafi ke ciki a jihar, Shugaban Ƙungiyar Makafi ta Ƙasa Reshen Jihar Kano, Malam Musa Kura ya soki gwamnati kan yin shakulatin ɓangaro da buƙatun masu buƙata ta musamamn waɗanda suka ƙunshi makafi, inda ya yi kira gare ta da ta tsaya wa masu buƙata ta musamamn su samu ilimi.
“A ƙasashen da suka ci gaba dukkan haƙƙoƙi da samar da walwala ga masu buƙata ta musamamn abin kiyayewa ne a wajen gwamnati.
“Zan iya tunawa an kakkafa kwamitoci iri-iri inda suka bayar da shawarwarin da za su bunƙasa rayuwar masu buƙata ta musamman, sai dai har yanzu gwamnati ba ta aiwatar da waɗanan shawarwari ba,” in ji shi.
Ya ce akwai buƙatar a bai wa masu buƙata ta musamman dama don su nuna irin baiwar da Allah Ya yi musu kuma hakan zai iya bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.
Ya ce ya kamata a riƙa tallafa musu musamman idan suka nuna sha’awar son ci gaba da karatunsu.
Ya kuma roƙi gwamnati ta sake buɗe musu cibiyoyin koyar da sana’o’i domin mutanensu su koyi sana’o’in da za su dogara da kansu.
Kuma gwamnati ta ba su jari wajen fara sana’o’in inda ya ce wata rana za su bunƙasa har gwamnati ta amfana domin za su riƙa biyan haraji tare da samar da aikin yi ga wasu.
Ya ce, “Muna da cibiyoyi a ƙananan hukumomi 44 na jihar nan, abin da ya rage wa gwamnati shi ne ta gyara su tare da zuba musu kayan aiki don mutanenmu su samu abin dogaro da kansu a cikin al’umma.
“Muna so gwamnati ta ƙirƙiro mana ma’aikata sukutum da za ta riƙa kula da buƙatunmu sannan idan an tashi bayar da shugabancin hukumar ya zama an bayar ga ɗaya daga cikinmu.”
Malam Musa Kura ya kuma zargi al’umma da jefa masu buƙata ta musamman a cikin bara, inda ya ce, “Da zarar an haifi wani da wata lalura ko ta same shi daga baya, to, sai ki ji mutane na cewa sai dai ya yi bara.
To da haka ake cusa wa mutum ra’ayin bara ko da kuwa bai yi niyya ba,” in ji shi.
Dokta Ali Tamasi Mu’az malami ne a Sashen Ilimin Masu Buƙata ta Musamman a Kwalejin Shari’a da Addinin Musulunci ta Malam Aminu Kano ya bayyana cewa akwai buƙatar masu buƙata ta musamman su canza tunaninsu da kuma halayyarsu don su taimaki kansu da kuma gwamnati.
Ya ce, “A haƙiƙanin gaskiya gwamnati tana iya ƙoƙarinta, domin ta mayar da ilimin masu buƙata ta musamman kyauta a jihar.
“Yanayin ba zai canza ba idan su masu buƙata ta musamman ba su canza halayyarsu da tunaninsu ba.
“Ya kamata su bar harkar bara kwata-kwata, su samu wata sana’a su riƙa yi domin su dogara da kansu a cikin al’umma.”