Makaho bai san ana ganinsa ba…
Bisa ga dukkan alamu dai tura ta kai bango, domin kuwa jama’an Arewa sun fara yunkurowa don magance matsin da ake yi masu a kasar da aka mayar da su ‘ya’yan bora, ana take hakkokinsu yadda aka ga dama, a kuma buge su , a hana su kuka. kungiyar Fitattun mu ‘Yan Arewa da ake […]
Bisa ga dukkan alamu dai tura ta kai bango, domin kuwa jama’an Arewa sun fara yunkurowa don magance matsin da ake yi masu a kasar da aka mayar da su ‘ya’yan bora, ana take hakkokinsu yadda aka ga dama, a kuma buge su , a hana su kuka. kungiyar Fitattun mu ‘Yan Arewa da ake kira Arewa Consultatibe Forum, ACF ta fara rubuta wata zungureriyar wasika ga Shugaban kasa, Goodluck Jonathan don su nuna masa suna sane da lusarinsa da kuma yadda ya bayar da dama ana yi wa Arewa cin kashi da kuma yadda ake yi wa jama’ar cikinta cin fuska ba gairan, ba dan dalili. A takaice dai ana iya cewa ‘ya’yan wannan kungiyar sun nuna rashin gamsuwarsu da yadda gwamnatin Jionathan ke yi wa al’amuran da suka shafi tsaron kasar nan rikon sakainar kashi, musamman ma yamutsin Boko Haram a shiyyar Arewa-maso Gabashin kasar nan.
A cikin wannan wasikar wacce shugaban kungiyar, Alhaji Ibrahim Comassie, Sardaunan Katsina da kuma Sakatarenta, Mr. J. Ubah suka sanya wa hannu, fitattun ‘yan Arewar sun ji takaicin yadda Shugaba Jonathan ya kawar da kansa daga irin ta’asar da ake aikatawa a yankin Arewa, inda ‘yan Boko Haram ke cin karensu ba babbaka tun misalin shekaru biyar da suka shude, suna ta kisan kai ba kakkautawa, suna kokkona gidaje da dukiyoyin bayin Allah da kuma muzgunawa bayin Allah wadanda ba su ji, ba su gani ba.
kungiyar ACF ta yi mamakin ganin duk da dokar-ta-bacin da aka kafa a jihohin Barno da Yobe da Adamawa har yanzu ana kakkame wasu muhimman garuruwa da kauyuka, sa’annan kuma an ki gaggauta daukar matakan da suka da dace don taka wa ‘yan ta’addan birki, kuma halin ko’in-kula (adankiya – I don’t care or carefree attitude, in ji turawan Ingilishi) da Shugaba Jonathan ya nuna game da mawuyacin halin da ‘yan matan makarantar Chibok ke ciki na da ban takaici matuka, domin kuwa ya nuna babu abin da ya dada shi da kasa gami da haka, hankali ya fi ta’allaka wajen tsara dabarun zarce bisa mulki ko ana ha-maza-ha-mata.
Dangane da haka kungiyar ta lissafa wasu ka’idoji guda uku da ta wajabta wa Shugaba Jonathan yin aiki da su, don kawo karshen tashin-tashinar ‘yan kungiyar Boko Haram. Da farko dai tilas ne ya turza wajen hana ‘yan ta’addar ci gaba da mamaye garuruwa, ya kuma ja damarar fuskantarsu don a yi ta a gama. Haka nan kuma tilas ne ya kafa wani kwamitin da zai binciki zargin da wani Baturen kasar Australiya, Dokta Stephen Dabies ya yi wa Sanata Ali Modu Sheriff, tsohon Gwamnan Jihar Barno da tsohon hafsan-hafsoshin sojin Najeriya, Janar Azubuike Ihejirika da wasu mutanen da bai fayyace ba game da daure wa ‘yan ta’addar gindi da taimaka masu da kayayyakin tayar da kayar baya. Sa’annan kuma ‘ya’yan kungiyar sun nemi a hanzarta yim amfani da rahoton kwamitocin Sheik Ahmed Lemu da na Gaji Galtimari da kuma na Tanimu Turaki, wadanda aka kakkafa don gano bakin zaren warware matsalolin Boko Haram.
Ita dai wannan kungiyar ta ce ya wajaba ne a gare ta ta rubuta wannan takardar, domin kuwa jama’ar shiyyar Arewa-maso-Gabas sun damu matuka game da yadda ake yi masu yankan rago, ana kuma yi wa mata fyade, ga shi nan kuma an jefa jama’ar birnin Maiduguri cikin kunci, tun daga lokacin da aka kakkarya dukkan gadojin da za a iya bi a je garin daga kowace kusurwa. Dangane da haka mutanen Arewa ke cewa da gangan ne aka tsiri wannan shegantakar da sunan Boko Haram don a ga bayan Arewa, a kuma kai ta kasa idan aka yi nasarar gurgunta tattalin arzikinta da kuma daidaita jama’arta.
A takaice dai ana iya cewa wannan kungiya ta ACF ta wanke wa gwamnatin Shugaba Jonathan hannu a kai, ta kuma dawo daga rakiyarta, domin kuwa jama’ar Arewa sun dade da sanin cewa wannan gwmnatin ba ta da wani amfani a gare su, ba kuma za ta iya kare masu mutunci da hakkokinsu ba. Dalilinsu kuwa shi ne hukumomi da ma’aikatan gwamnati ba su iya tabuka komai don tserar da su daga ja’ibar da aka dulmuya su a ciki.
Babu inke ko wai a cikin furucin wannan kungiya domin kuwa ga shi nan kiri-kiri Shugaba Jonathan ya kasance tare da Modu Sheriff, mutumin da ake zargi game da daure wa Boko Haram gindi, a wata ziyara da ya kai wa Shugaban kasar Chadin da ita ma ake zargi da masaniya game da tabargazar da kungiyar ke haddasawa a Najeriya, kuma kamar yadda ake cewa, tare da taimakon sojojinta. Amma Shugaba bai yi ko gezau ba, duk da kururuwar da ake ta shirgawa game da bala’o’i da fitintinun ta’addanci ke haddasawa a kasar nan.
A yanzu dai ‘Yan Arewa sun gasgata zargin da ake yi cewa yaki ne ake yi da Arewa don a gurgunta ta, tun da dai har yanzu ana nan ana ta kashe-kashe ba wanda ya isa ya hana, kuma abin ma sai karuwa yake ta yi, ba ranar tsagaitawa balle a ce an kawo karshe. Abin dai tamkar da biyu ne ake yi: don a yaki al’ummar Arewa da sunan addininsu, a kuma idar da burin ganin an yi fata-fata da Arewar don kada ta ci gaba da yin tasiri a harkokin siyasa da na mulkin kasar nan. Shi ke nan, kada ka kara, kada ka raga. Yanzu dai an an rigaya an taba makaho a kafada, ya san ana ganinsa, sai ya shiga taitayinsa.