Makaho na neman zama dan majalisar Adamawa

Wani makaho mai suna Kwamared Muhammad Ardo Gombi ya yanki tikitin tsayawa takarar domin wakiltar mazabar Gombi da Hong a Jihar Adamawa a Majalisar Tarayya. Makahon mai son tsayawa takara a karkashin Jam’iyyar APC, ya shaida wa manema labarai a Yola cewa ya samu karfin gwiwar fitowa takarar ce kan yadda ya sami goyon baya […]

Makaho na neman zama dan majalisar Adamawa
Makaho na neman zama dan majalisar Adamawa

Wani makaho mai suna Kwamared Muhammad Ardo Gombi ya yanki tikitin tsayawa takarar domin wakiltar mazabar Gombi da Hong a Jihar Adamawa a Majalisar Tarayya.

Makahon mai son tsayawa takara a karkashin Jam’iyyar APC, ya shaida wa manema labarai a Yola cewa ya samu karfin gwiwar fitowa takarar ce kan yadda ya sami goyon baya daga jama’ar mazabarsa.
Kwamared Ardo Gombi ya kara da cewa duk da cewa yana da nakasar ido, abin ya ba shi mamaki shin ne yadda jama’a suka neme shi ya tsaya takarar. Ya ce jin dadin hakan ya sa ya yi na’am da kiransu kuma yana fatar samun goyon baya daga shugabannin jam’iyyar musamman tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar. Ya ce “Abin ya ba ni mamaki matuka amma na bar komai ga Allah don haka ina mai neman goyon baya da hadin kai musamman daga tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar.”
Ya ce zai iya karfinsa ya ga ya taimaka wa jama’a, musamman abubuwa da suka shafi bunkasa harkar noma da ruwan sha da gyaran hanyoyi. “Idan aka zabe ni, ba zan yi wata-wata ba wajen bullo da dokokin da za su daga darajar mu nakasassu domin kuwa an bar mu a baya.”