Makaho ya zo na biyu a gasar musabakar Izala reshen Jihar Filato

Wani matashi makaho mai suna Tanimu Usman da ya fito daga karamar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato ya zo na biyu a musabakar karatun Alkur’ani Mai girma karo na 17 da kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Ikamatis Sunnah reshen Jihar Filato ta gudanar a garin Jingir.Wanda ya zamo gwarzon shekara a gasar, shi […]

Makaho ya zo na biyu a gasar musabakar Izala reshen Jihar Filato

Sheikh Sa'idu Hassan Jingir yana gaisawa da makaho Tanimu Usman wanda yazo na biyu a gasar karatun Alkur'ani ta Jihar FilatoWani matashi makaho mai suna Tanimu Usman da ya fito daga karamar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato ya zo na biyu a musabakar karatun Alkur’ani Mai girma karo na 17 da kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Ikamatis Sunnah reshen Jihar Filato ta gudanar a garin Jingir.
Wanda ya zamo gwarzon shekara a gasar, shi ne Alhassan Yunusa Muhammad daga karamar Hukumar Kanam, yayin da Adam Ibrahim Adam shi ma daga karamar Hukumar Kanam, ya zo na uku.
Da yake jawabi a wajen rufe gasar Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar ta kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir, ya yi kira ga matasa kan su dauki wannan makaho ya zama darasi a gare su. “Wannan bawan Allah makaho, Allah Ya debe masa gani na ido ya bar masa gani na zuciya da tunani mai kyau, ga shi har ya haddace Alkur’ani Mai girma. A yayin da akwai miliyoyin mutane masu gani amma  da kyar wani zai iya karanta wani abu a cikin Alkur’anin,” inji shi.
Sheikh Jingir ya ce addinin Musulunci ba addini ne na ragwanci da barace-barace ba, addini ne na aiki. Ya ce da wannan bawan Allah ya tsaya a bara ba zai iya haddace Alkur’ani ba.
Sheikh Jingir wanda mataimakin shugaban majalisar na biyu kuma Sa’in kungiyar na kasa Sheikh Sa’idu Hassan Jingir ya wakilta, ya ce Boko Haram karya ne. Don haka ya yi kira ga jama’ar Musulmi kan su tashi a rungumi karatun boko domin mu zamo likitoci da sojoji da injiniyoyi da ’yan sanda da kuma kasancewa kwararru a sauran fannonin rayuwa.
Sai ya yi kira ga wadanda suka shiga takarar kan su yi aiki da abubuwan da suka karanta. Ya ce ba a kirga mai ilmi a cikin masu ilimi, sai wanda yake aiki da ilimin da yake da shi. Kuma ya yi kira ga jama’a su zauna lafiya da juna su guji aikita miyagun laifuffuka, kuma su rungumi noma da kiwo da sana’a.
A jawabin dan Majalisar Jihar Filato, mai wakiltar mazabar Pengana Mista Musa Gonduna ya ce al’ummar Musulmi da Kiristan mazabarsa ba sa nuna kyama ga juna, shi ya sa duk abin da ya taba wani daga cikinsu sukan dauka ya taba su ne baki daya. Don haka ya yi kira ga al’ummar Najeriya su yi koyi da al’ummar mazabar.Ya ce idan babu zaman lafiya addinin ma, ba za a iya gudanar da shi ba, don haka kada jama’a su yi wasa da maganar zaman lafiya.
Tun farko a jawabin Ko’odinetan shirya gasar Ustaz Umar Ahmed Munka’ilu, ya ce gasar karo na 17 an yi kwanaki hudu ana gudanar da ita, kuma ’yan takara 107 da suka fito daga kananan hukumomin jihar ne suka fafata.