Makahon da ke sana’ar POS

Ina da mata daya da ƙananan yara guda biyu kuma gaskiya ina son su yi karatu duka na addini da na boko.

Makahon da ke sana’ar POS

Isyaku Mahmud, makaho ne dan shekara 28 da ke sana’ar sayar da data a yankin Kudancin Kaduna.

Ya shaida wa Aminiya cewa har sana’ar hada-hadar kudi ta POS yana yi a baya, amma yanzu ba shi da jari.

Aminiya ta ga yadda makahon yake sarrafa manhajojin WhatsApp is Fesbuk kuma yake sayar da data kai tsaye daga wayarsa ta hanyar amfani da tsarin Smart Cash tare da tura kudi da wayar tasa, kamar yadda ya gwadawa wakilinmu.

Dan asalin garin Yalwa da ke Karamar Hukumar Tudun Wada (Dan Kadai) da ke Jihar Kano ne, ya kwashe shekaru kusan biyar yana zuwa yawon bara a garin Kafanchan da ke Jihar Kaduna.

Aminiya ta samu zantawa da shi, inda ya gwada duk abubuwan da yake yi da wayarsa ciki, har da lalubo wakar da ya yi ya kuma tura cikin wani zaure na mawaƙa ba tare da wani ya nuna masa ko ya taimaka ba.

Yana iya kuma tattaunawa da kowa ta hanyar sauti a manhajar WhatsApp tunda bai iya rubutu ba.

Amma da kansa yake budewa ya lalubo wanda yake son tura wa da sako kuma ya tura masa.

“Ka san ina yin wakokin yabon Manzon Allah. Idan na samu ƙarin baitin sai na ɗauko wayata na rera tunda ba zan iya rubutawa ba.

“Idan na gama hada adadin baitukan da nake so akwai dalibai ’yan Islamiyya, sai na ba su muje inda ake buga wakoki a studiyo, sai su hau su rera.

“Ba ni nake rerawa ba, amma duka wakokina ne. A can garinmu nake wannan kuma a yanzu haka ina da kasidu da aka buga sun haura guda 20.

“An haife ni ne a shekarar 1997, an shaida min cewa an haife ni da idanu na garai, amma bayan an yaye ni, a shekarar sai mahaifiyata ta rasu kuma tun daga nan sai na daina gani, wato na makance, shine har zuwa yau kuma,” in ji shi.

Ya ce ya yi karatun tsangaya kafin daga baya aka matsa masa cewa sai ya fita yawon bara.

“Saboda haka ba a son raina nake bara ba, amma a lokacin babu wani abu da zan iya yi. Wannan ya faru ne a shekarar 2012 tun lokacin nake bara.”

Ya ce da zai samu wani tallafi na jari, a shirye yake ya yi wasu sana’o’i ko buɗe shagon harkar POS ko wani abu da zai iya dogaro da shi musamman yanzu da yake da yara ƙananan guda biyu da yake son su samu kulawa ta musamman tare da yin karatu mai zurfi.

“Ina da mata daya da ƙananan yara guda biyu kuma gaskiya ina son su yi karatu duka na addini da na boko.”

Tags