Makaman Yaki na Kirista (1)
A yau bisa ga yardar Allah Mai iko duka, za mu soma bincike ne a kan Makaman Yaki irin na Kirista, wato masu bin Yesu Kiristi Ubangijinmu da Mai cetonmu. Eh, yau muna cikin mawuyacin zamani, mugunta iri-iri, gaba tsakanin ’yan uwa, a kullum kuwa muna fuskantar kalubale daga wurin makiya da suke kewaye da […]
A yau bisa ga yardar Allah Mai iko duka, za mu soma bincike ne a kan Makaman Yaki irin na Kirista, wato masu bin Yesu Kiristi Ubangijinmu da Mai cetonmu. Eh, yau muna cikin mawuyacin zamani, mugunta iri-iri, gaba tsakanin ’yan uwa, a kullum kuwa muna fuskantar kalubale daga wurin makiya da suke kewaye da mu da hare-hare daban- daban da muke fama da su. Wannan ba abin da za mu dauke shi da sakaci ba ne ko kadan. Dole ne mu san wane irin yaki ne muke fuskanta a matsayinmu na masu bin Yesu Kiristi, wane irin makamai ne ya kamata mu dauka domin kare kanmu, wane iri mataki ne kuma za mu dauka domin mu iya cin nasara bisa magabcin da ya kawo mana hari?
Yawanci masu bin Yesu Kiristi suna shiga irin wannan yaki ba tare da la’akari da wadannan makamai ba, shi ya sa suna shan hasara, kuma a kullum magabcin yana cin nasara a bisa kansu. Idan har muna so mu ci nasara bisa wanda ya fito domin ya fuskance mu a filin yaki, ya zama mana dole ne mu yafa makamai na yakin nan; mu kuma zo gaban Allah Mai iko duka domin Ya koya mana yadda ya kamata mu fito filin daga da cikakken shiri. MaganarSa tana koya mana a cikin Littafin Samaila na Biyu, sura ta 22, aya ta talatin da biyar – (2Samaila 22: 35) “Yana koya (wa) hannuwana su yi yaki; Har damatsuna suna tausa baka ta jan karfe.” Dole ne mu zo ga wannan matsayi na barin Ubangiji Allah Ya koya mana yadda mutum zai yi wannan yaki ya kuma ci nasara.
Kafin wani ya yi tambaya ko wani irin yaki ne nake nufa? Kuma mene ne kayan yakin? Bari in yi bayani kadan daga cikin Littafin Rai wato maganar Allah ke nan kamar yadda ya ba mu ita – a cikin Littafin 2Korinthiyawa 10 : 3 – 7; a wannan wuri maganar Allah na cewa “Gama ko da muna tafiya cikin jiki, ba mu yi yaki bisa ga jiki ba, (gama makaman yakin namu ba na jiki ba ne, amma masu iko ne gaban Allah da za su rushe wurare masu karfi); muna rushe zace-zace da kowane madaukakin abu wanda aka daukaka domin gaba da sanin Allah, muna komowa da kowane tunani cikin bauta ga biyayyar Kiristi, muna shiri fa mu dauki fansa bisa dukan kangara, sa’ar da biyayyarku ta cika. Kuna lura da abin da ke gaban fuskarku? Idan kowa yana amincewa da kansa, bari ya sake lura da wannan a ransa kuma, kamar yadda shi na Kiristi ne, mu kuma haka nan.”
Mu gane wannan sosai, akwai yaki kashi biyu, na farko shi ne wanda ido zai iya gani, kunne zai iya jin amon bindiga, za ka iya ganin wadanda suke harbi da bindigar da dai sauransu. Yin amfani da manyan makamai na yaki har da jiragen sama da makamantansu. A yau irin wannan yakkin ne mutane da yawa suka sani, yaki na jiki ke nan; yaki tsakanin kasa da kasa ko tsakanin kasashe, irin wannan yakin ba komai ba ne idan muka duba yaki na biyu.
Yaki na biyu shi ne – Yaki na ruhaniya; wannan shi ne mafi wahala domin dagar yakin tana cikin zuciyarka, domin wannan ma makaman yakin ba za su taba zuma na jiki ba kamar bindiga, takobi, manyan makamai na karfe na zamani. Makaman wannan yaki, makamai ne na ruhi, wadanda idon mutum ba zai iya gani ba domin wadannan makamai na ruhi ne wadanda idan har mun gane yin amfani da su, za mu yi rayuwa wadda za ta gamshi Allah a koyaushe. Mu sani fa cewa duk inda ake yaki; dole akwai magabci wanda ake yaka, tun a yanzu; bari mu sani cewa, masu bin Yesu Kiristi, muna da magabci daya kawai kuma da shi kadai muke yaki, kuma wannan yaki zai ci gaba har sai mun sadu da Ubangijinmu da mai cetonmu Yesu Kiristi. Wannan magabcin kuwa Shaidan ne da kansa; idan kuwa muna so mu yaki Shaidan har mu iya cin nasara, dole ne mu dauki wadannan makamai mu kuma tsaya da karfi. A cikin Littafin Afisawa 6: 10 – 18 maganar Allah na koya mana mu yafa wadannan makamai idan dai muna so mu ci nasara a kan Shaidan. “Daga bisani, ku karfafa cikin Ubangiji, cikin karfin ikonsa kuma. Ku yafa dukkan makamai na Allah, domin ku sami ikon da za ku yi tsayayya da dabarun Shaidan. Gama kokuwarmu ba da nama da jini take ba, amma da mulkoki da ikoki da mahukuntan wannan zamani mai duhu da rundunai masu ruhaniya na mugunta cikin sammai. Domin wannan fa, ku dauki dukkan makamai na Allah da za ku iya tsayayya cikin mugunyar rana, kuma bayan da an gama duka, a tsaya. Ku tsaya fa, kun rigaya kun daure gindinku da gaskiya, kun yafa sulke na adalci, kun daura wa sawayenku shirin bishara ta salama; masamman kuma, ku dauki garkuwa ta ban-gaskiya, wadda za ku bice dukan jefe-jefe masu wuta na mugunta, ku dauki kwalkwali na ceto kuma da takobin ruhu wato maganar Allah: kuna addu’a kowane lokaci da kowace irin addu’a da roko; kuna tsare wannan da iyakar naciya da roko saboda dukan tsarkaka.”
Irin wannan yaki ba na nama da jini ba ne, wannan shi ne abin da dukan masu bin Yesu Kiristi suke fuskanta a yau da kullum. Za mu zo mu gane cewa, idan wani bai iya cin nasara a cikin ruhaniya ba, a kullum ne zai kasa ga darajar Ubangiji Allah domin ba zai samu cikakken karfin da zai yi gwagwarmaya da Shaidan ba. Haka nan a koyaushe ba zai iya kare kansa ba, Shaidan zai fi karfinsa. Abu guda da ya zama kamar dole ga kowane mai bin Yesu Kiristi shi ne idan har mutum yana so ya ci nasara bisa Shaidan-lallai ne ya san wannan makamai na Allah. Tushen karfin kowane mai bin Yesu Kiristi cikin ruhaniya shi ne sanin Allah.
Idan Allah Ya yarda za mu yi bincike sosai domin mu gane irin wannan yaki da muke fuskanta a yau da kullum, mu kuma san matakan da za mu dauka domin wadannan jerin makamai su yi mana aiki. Mu ci gaba da rokon Allah domin Ya ba mu zaman lafiya cikin wannan kasa tamu Najeriya, amin.