Makaman yaki na Kirista (22)

A yau, ina so ne mu yi bincike a kan yadda Yesu Kristi ya sha wahala domin ceton mu. A cikin littafin Filibiyawa 2 : 5 – 11, maganar Allah tana cewa “Ku kasance da wannan hali a cikinku wanda ke cikin Kiristi Yesu kuma, Shi da shi ke cikin Surar Allah, ba ya maida […]

Makaman yaki na Kirista (22)
Makaman yaki na Kirista (22)

A yau, ina so ne mu yi bincike a kan yadda Yesu Kristi ya sha wahala domin ceton mu. A cikin littafin Filibiyawa 2 : 5 – 11, maganar Allah tana cewa “Ku kasance da wannan hali a cikinku wanda ke cikin Kiristi Yesu kuma, Shi da shi ke cikin Surar Allah, ba ya maida kasancewarsa daidai da Allah abin rairaito ba, amma ya wofinta kansa da ya dauki surar bawa, yana kasancewa da surar mutane: da aka iske shi cikin kamanin mutum, ya kaskantar da da kansa, ya zama yana biyayya har da mutuwa, i, har mutuwa ta gicciye. Domin wannan, Allah ya ba shi mafificiyar daukaka, ya ba shi suna wanda ke bisa kowane suna; domin cikin sunan Yesu, kowace gwiwa ta rusuna, ta cikin Sama da ta kan duniya da ta karkashin duniya, kowane harshe kuma shi shaida Yesu Ubangiji ne. zuwa darajar Allah Uba.” 

Mu duba kuma cikin Littafin Ishaya 53 : 1 – 12 wadda take cewa, “Wanene ya gaskanta abin da muka ji? Ga wanene kuma hanun Ubangiji ya bayana? Gama ya yi girma a gabansa kamar dashe mara kwari, kamar saiwa a cikin busasshiyar kasa: ba shi da wani fasali, ba ko dadin gani gare shi; sa’dda mun dube shi, ba wani jamali gare shi da za mu so shi ba. Abin raini ne, yasasshe a wurin mutane, mai bakin ciki ne, ya saba da chiwuta: aka rena kamar wanda mutane suka kawar masa da fuska, mu kuma ba mu maishe shi wani abu ba. Lallai da kayan chiwutanmu ya nawaita, ya dauki bakin cikinmu, amma muka maishe shi bugagge, dukakke na Allah, mai shan wuya ne. Amma sabili da laifofin mu ne aka yi masa rauni, aka kuje shi domin kurakuranmu, foro kuma mai kawo lafiyarmu a kansa yake, ta wurin dukansa da ya sha mun warke. Dukkan mu kamar tumaki muka bata, kowane dayan mu mu karkata garin bin nasa tafarki; Ubangiji kuma ya dibiya masa dukkan kurakuranmu. Aka wulakance shi, duk da haka ya yi tawali’u, ba ya bude bakinsa ba, kamar dan rago da ake kaiwa wurin yanka, kamar yadda tumkiya wurin masu sosayanta take shiru.
Haka nan ba ya bude bakinsa ba. Bisa ga rashin gaskiya a shari’a aka kawar da shi, don mutanen zamaninsa fa. Wane ne a cikin su ya lura aka datse daga kasar masu rai? sabili da laifofin mutanensa aka buga shi. Tare da masu mugunta aka yi masa kabari, tare da mawadaci yake cikin mutuwassa kuma; gama ba ya yi zilama ba, ba ko karya a bakinsa ba. Amma Ubangiji ya nufa a kuje shi; ya sa masa azaba, lokacin da za ka maida ransa hadaya domin zunubi, za ya ga zuriyarsa, za ya tsawanta kwanakinsa, nufin Ubangiji kuma za ya yi albarka a cikin hannunsa. Za ya ga wahalar Ransa, zuciyassa za ta kwanta kuma, ta wurin sanin sa kuma bawana mai adilci za ya baratadda masu yawa. Za ya dauki kurakuransu kuma. Domin wannan fa zan bashi rabonsa tare da manya, za ya raba ganima kuma tare da karfafa, domin ya tsiyaye ransa har ga mutuwa, aka lissafta shi wurin masu laifi, duk da haka ya dauki zunubi na mutane da yawa, ya kuma yi roko sabili da masu laifi.”