Makaman Yaki na Kirista (3)

JIKI: Wannan jiki da muke dauke da shi, yana da sha’awoyi daban-daban da ba lallai ba ne irin wannan sha’awar jiki da na ido su zama abubuwan da za su gamsar da Allah ba. Yawancin lokaci Shaidan yakan  kawo su ne domin ya mallaki zuciyar mutane ya kuma janye tunaninsu daga bauta wa Allah Madaukakin […]

Makaman Yaki na Kirista (3)
Makaman Yaki na Kirista (3)

JIKI: Wannan jiki da muke dauke da shi, yana da sha’awoyi daban-daban da ba lallai ba ne irin wannan sha’awar jiki da na ido su zama abubuwan da za su gamsar da Allah ba. Yawancin lokaci Shaidan yakan  kawo su ne domin ya mallaki zuciyar mutane ya kuma janye tunaninsu daga bauta wa Allah Madaukakin Sarki ya kafa tunaninsu a kan kayan duniya. Idan ya ci nasara a bisa mutum haka nan, sai ka ga cewa mutum ya manta da Allah, ya manta cewa akwai mutuwa, ya manta cewa akwai gobe. Shi ya sa Ubangiji Allah Ya koya mana a cikin Littafin 1Yohanna 2: 15 – 17, inda maganar Allah take cewa:
“Kada ku yi kaunar duniya, ko abubuwan da ke cikin duniya, idan kowa ya yi kaunar duniya, kaunar Uba ba ta cikinsa ba. Gama dukan abin da ke cikin duniya da kwadayin jiki da sha’awar idanu da darajar rai ta wofi, ba na Uba ba ne, amma na duniya ne. Duniya ma tana wucewa duk da sha’awatata, amma wanda ya aikata nufin Allah ya zauna har abada.”
Mu gane wannan sosai, domin kuwa Shaidan yana amfani da wadannan hanyoyi a hankali har sai ya sa mutum ya manta da Allah, ya yi abin da ya ga damar yi. Dukan abin da zai sa mutum ya manta da Allah, wancan abin, abin gaba ne kwarai. Abin da zai raba mutum da Allah ba abin wasa ba ne ko kadan, Shaidan shi ne uban yaudara, a lokacin da zai kawo wa mutum ra’ayin yin wani abin da zai sa Ubangiji Allah Ya yi fushi da shi, zai mai da shi kamar wani abu wanda zai taimake ka. Mu dauki misali, kai ma’aikaci ne na gwamnati, kana da mukami babba a wurin aikinka, sai ya zamana cewa ta hanunka ne kudi masu dimbin yawa suke shiga da fita, abin da Shaidan zai yi shi ne ya nuna maka hanyoyi daban- daban da za iya bi ka saci kudin nan, ka azurta kanka da shi, a lokacin da kake wannan satar; ba zai kasance kamar sata ba ne, a’a, zai zama ne kamar Allah Ya ba ka sa’a, al’hali kuwa aikin zamba ne kake yi. Ko kuwa mu dauka zina, idan mutum ya saci kudi ko na gwamnati ko kuwa na wani, a lokacin mai yiwuwa ne ka ce kana jin dadi domin sauran mutane za su ga kamar kai mai kudi ne ashe ba su sani ba, kai babban azzalumi ne mai cin amana, haka nan da dukan sauran zunubi; dukansu za su raba mu da Allah, sai mu lura sosai, domin duk abin da zai raba mu da ganin Allah dole ne mu yake shi da dukan karfin da Allah Ya ba mu. A cikin Littafin 1Bitrus 2: 11 maganar Allah na koya mana cewa:
 “kaunatattu, ina rokonku misalin saukakku, baki masu tafiya kuma, ku hanu daga sha’awoyi na jiki wadanda ke yaki da rai.”
Zamanmu cikin wannan duniya na dan lokaci ne kawai. Ba za mu dauwama a wannan duniya ba; duniyar nan da kanta ma ba za ta dauwama ba, muna rayuwa cikin wannan duniya a misalin saukakku ne, baki wadanda da suke kan tafiya; kuma rana tana zuwa wadda Ubangiji Allah da kanSa zai zo domin ya kai mu ainihin mazauninmu tare da shi. Sha’awoyin jiki a kullum za su yi gaba da nufin Allah a cikin rayuwarmu; shi ya sa dole mu yi tsayayya da dukan irin wadannan abubuwa su gina katanga tsakaninmu da Allah. A cikin Littafin Galatiyawa 5: 17, maganar Allah na koya mana cewa “Gama jiki yana sha’awa gaba da ruhu; ruhu kuma gaba da jiki; gama wadannan biyu gaba suke da junansu; domin kada ku aika abin da kuke nufa.”
Akwai magabtaka tsakinin Allah da sha’awar jiki, sai mu lura da lokacin da Shaidan ya turo kansa domin ya kawo maka hari. Abu na biye kuma shi ne:
DUNIYA: A cikin Littafin Yohanna 16:31-33: Yesu Kiristi da kansa ya ce wa almajiransa kamar haka: “Yesu ya amsa musu, ya ce, Yanzu kun ba da gaskiya?, Ku duba fa, sa’a tana zuwa, har ma ta zo, inda za ku warwatse, kowa zuwa nasa, za ku bar ni ni kadai: amma ba ni daya ba ne, gama Uba yana tare da ni. Wadannan abubuwa na fada muku domin a cikin na ku samu salama. A cikin duniya kuna da wahala; amma ku yi farin ciki, na yi nasara da duniya.”
Duniya a wannan wuri tana nufin irin halaye ne na ’yan duniya, al’ada wadda ba ya daukaka sunan Ubangiji Allah, duniya tana nufin abubuwan da a wannan duniya ne za ta kare, ba za mu iya kaiwa wurin Allah ba, misali kudi, gidaje, motoci, da sauran abin da za ka iya samu domin kanka a wannan duniya. Idan mun iya ganewa da hanyoyin da Shaidan ya iya bi domin ya kawar da tunanin mutum daga bauta cikin gaskiya, za mu iya cin nasara a koyaushe a kansa, amma yawancin lokaci sai ka ga kamar wani rufa ido yake yi wa mutane ya rude su har su manta cewa akwai Allah ko kuwa akwai mutuwa idan ma an ki jin tsoron Allah. Sai mu tunani fa kwarai da gaske. Yesu Kiristi ubangijinmu ya ce mana a cikin wannan duniya akwai wahala, sai ya sake cewa, mu yi farin ciki domin ya riga ya ci nasara bisa duniya. Lokacin da Yesu Kiristi ya shigo cikin wannan duniya a kamannin mutum, Shaidan ya yi iya nasa kokari domin kada shi, ya jarabce shi ta kowane fanni, amma Shaidan bai iyacin nasara bisa Yesu Kiristi ba ko kadan.
Za mu kara bayani a kan wannan idan Allah Ya bar mu cikin masu rai mako mai zuwa. Ubangiji Allah Ya taimake mu, amin.