Makaman Yaki na Kirista (5)
Yadda ake yin wannan yaki:A koyarwar da muka yi a baya, mun tsaya ne a kan yadda wannan yaki cewa yana somawa ne cikin tunaninmu, Shaidan yakan shuka nasa ra’ayi cikin zuciyar mutum, sai ya bar shi da sauran tunani – ko ya aikata ko kuwa ya ki aikata abin da Shaidan yake so ya […]
Yadda ake yin wannan yaki:
A koyarwar da muka yi a baya, mun tsaya ne a kan yadda wannan yaki cewa yana somawa ne cikin tunaninmu, Shaidan yakan shuka nasa ra’ayi cikin zuciyar mutum, sai ya bar shi da sauran tunani – ko ya aikata ko kuwa ya ki aikata abin da Shaidan yake so ya yi. Ainihin wurin kokuwar kuwa cikin zuciyar mutum ne kamar yadda muka gani a cikin Littafin 2Korinthiyawa 10 : 4 – 6 wadda take cewa, “Gama makaman yakin namu ba na jiki ba ne, amma masu iko ne gaban Allah wadanda za su rushe wurare masu karfi; muna rushe zace-zace da kowane madaukakin abu wanda aka daukaka domin gaba da sanin Allah, muna komo da kowane tunani cikin bauta ga biyayyar Kiristi, muna shiri fa mu dauki fansa bisa dukkan kangara, sa’ar da biyayyarku ta cika; mu sani fa cewa yaki koda na cikin wannan duniya yakan soma ne da tunani da Shaidan ya shuka a cikin zuciyar dan Adam.
Da zarar wannan tunani ya soma kuwa, idan har ba mu iya cin nasara a lokacin ba, babu shakka Shaidan zai ci nasara bisa kan kowane dan Adam. Irin wadannan tunani suna zuwa ne kamar jaraba, jaraba kuwa shawara ce da Shaidan yakan kawo wa mutum domin ya yi wa Allah rashin biyayya. Idan har mutum ya yarda ya bi shawarar da Shaidan ya ba shi, to ya aikata zunubi ke nan, Shaidan ba zai taba ba ma mutum shawara ya yi abin da zai gamsar da Allah ba ko kadan; sai mu yi tunani game da rayuwar da muke yi, mu lura da irin tunanin da muke bari ya shigo mana cikin zuciya har ya samu wuri su tsira su kuma yadu. Allah Ya ba mu iko mu iya cin nasara bisa zuciyarmu, a koyaushe idan Shaidan ya zo da jarabawarsa, muna da ’yanci mu ki karba; balle ma a ce mu yi aiki da shi.
Daga ina mu ke samun karfin yin wannan yaki?:
A cikin Littafin Afisawa 6: 10, maganar Allah tana cewa, “Daga bisani; ku karfafa cikin Ubangiji, cikin karfin ikonSa kuma.” Mutum nama da jini ba zai iya yakar Shaidan da karfin tuwo ba, domin Shaidan ruhu ne, yakarsa kuwa sai da karfin Ruhu. Maganar Allah na cewa mu karfafa cikin Ubangiji, cikin karfin ikonSa kuma, dole ne idan har muna so mu ci nasara cikin wannan yaki, mu dogara ga ikon da ke cikin Allah, wannan kuwa zai zamana ne kawai idan da gaske mun san wannan Ubangiji Allah. Makamai irin na duniya ba su da amfani a cikin irin wannan yaki, ainihin ikon da yake bayan wannan irin cakuna, Shaidan ne da kansa; shi ya sa ba za ka iya taba cin nasara a cikin irin wannan yaki da kayan fada na duniya ba. karfinmu dole ya zama cikin Ubangiji Allah. Idan Allah bai taimake ka ba, babu yadda mutum zai iya cin nasara. Akwai wata kalma da mutane sukan fadi, amma ban ga irin waccan magana a cikin Littafi Mai tsarki ba, maganar ita ce – Allah Ya ce, ka tashi in taimake ka. Babu magana haka a cikin Littafi Mai tsarki: mutane sukan yi magana kamar tana da ma’ana amma gaskiya ita ce, ba ta da ma’ana ko kadan, idan Allah Ya yi niyyar taimakon mutum, ba Ya bukatar karfinka ko kadan, domin mutum zai iya cewa, da karfinsa ne ya aikata wannan abin ko wancan abin. Allah ba Ya gazawa ko kadan a cikin duk abin da Yake so Ya yi. A cikin wannan irin yaki da muke tattaunawa a kai kuwa, idan har muka iya yarda mu bar wa Allah Ya yi wannan yaki a madadinmu, babu shakka za mu ci nasara.
A cikin Litafin Afisawa 1 : 17 – 19, maganar Allah tana cewa, “Allah na Ubangijinmu Yesu Kiristi,Uban daraja, ya ba ku ruhu na hikima da na bayani cikin saninSa; idanun zuciyarku su haskaka, domin ku sani ko mene ne begen kiranSa, da ko mene ne wadatar darajar gadonSa cikin tsarkaka, da ko mene ne mafificin girman ikonsa zuwa gare mu, mu masu ba da gaskiya, gwargwadon aikin nan na karfin ikonsa.” Mutum nama da jini ba ya da iko ko karfin da zai yi yaki a madadin Allah. Mu da muka rigaya muka ba da gaskiya ga Allah Ubangijin ta wurin ceton da muka samu cikin Yesu Kiristi, mun rigaya mun shigo wani irin zumunci na ruhaniya tare da Allah Mahalicci, alkawarinsa zuwa gare mu kuma zai tabbata har abada abadin, mu da muke cikin ban-gaskiya mun samu wadata kwarai da gaske cikin Ubangijinmu Yesu Kiristi, babu abin tsoro kuma, babu abin fargaba, mun ba da gaskiya Allahn da muke bautawa Yana da iko Ya yaki domin kanSa, babu dabarar Shaidan wanda bai sani ba; idan har za mu yarda mu ba shi zarafi, to za mu ga irin ceton da zai kawo mana daga cikin hannuwan magabta. Mu tuna mun rigaya mun yi bincike a kan ko wane ne ainihin magabci: mun sani ba mutum ba ne ko da yake shi ainihin magabcin yana iya yin aiki da mutum; shi ya sa, duk lokacin da ka ga cewa akwai tsatsaguwa cikin jama’a wadanda suke zama tare na shekaru, ba wai wani abu bane a’a, Shaidan ne ya shigo cikin al’umma da tasa irin shawara, sai kuma daga cikin mutanen wurin suka yarda da irin waccan shawara da ke ainihin dalilinta dama ta raba tsakanin ’yan uwa ne. To irin wannan ba za a iya yakarta da kwari da baka ba, ko kuwa su bindiga kirar dan Adam, ko wuka da su takwabi ba, ba za ka taba cin nasara ba ko kadan.
Hanya daya kawai idan har za mu ci nasara; wato mu gane asirin karfin da muke da shi cikin Yesu Kiristi. Madogararmu ba kayan yakin wannan duniya ba ne, mun rigaya mun gane wadansu makaimai wadanda suka fi kowane irin kayan fada na wannan duniya. Idan Allah Ya yarda za mu soma duba daya bayan daya, mu ga yadda ake aiki da su. ’Yan uwana wannan yaki da muke ciki ba kamar yaki ba ne, yakin da ya isa ya sa ka kashe a duniya, kuma ka kasa samun rabo a wurin Allah bayan ka bar duniyar; ba abin da za ka dauke shi da wasa ba ne. Idan ba mu kula ba, mu tuna da abin da maganar Allah ke fadi a cikin Litafin 1Bitrus 5 : 8, “Ku yi hankali shimfide, ku yi zaman tsaro, magabcinku Shaidan, kamar zaki mai ruri, yana yawo, yana neman wanda zai cinye.” Kada ka yarda ka zama abincin Shaidan. Wani lokaci Shaidan yakan yi amfani da siyasa, ya yi wannan ruri, wani lokaci kuwa zai yi amfani da addini ya yi wannan ruri, idan har ba ka gane ba, to lallai zai cinye, kamar yadda rayukan mutane suka salwanta a cikin shekaru kadan da suka gabata. Sai mu yi lura kada Shaidan ya auko mana babu shiri. Ubangiji Ya taimake mu, amin.