Makaranta ta rushe da dalibai suna zana jarabawa a Jos

Benen mai hawa biyu ya rushe ne a yayin da dalibai ke zana jarabawa a safiyar Juma’a

Makaranta ta rushe da dalibai suna zana jarabawa a Jos

Ginin makarantar sakandaren Kent Academy ya rushe da dalibansa a yayin da suke rubuta jarabawa a garin Jos na Jihar Filato.

A halin da ake ciki dalibai da dama sun makale a cikin baraguzan ginin makarantar mai hawa biyu da ke unguwar Busa Buji a Karamar Hukumar Jos ta Arewa.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 11 na safiyar ranar Juma’a 12 ga watan Yuli, 2024.

Tuni jami’an tsaro da jami’an gwamnati da al’ummar gari suka isa wurin inda suka dukufa gudanar da aikin ceto daliban da abin ya ritsa da su.

Wakilinmu ya bayyana cewa an samu nasarar zakulo wasu daga cikin daliban, inda aka garzaya da wadanda suka samu rauni zuwa asibiti.

Ana kuma farganar samu asarar rai, amma ba a kai ga gano adadin ba, ko aka sanar a hukumance.

Karin bayani na nan tafe…….