Makarantar Al-Hidaya ta Mararaba ta yaye dalibai

Makarantar Islamiyya ta Al-Hidaya da ke garin Mararaba a Jihar Nassarawa ta yaye dalibanta da suka yi karatu a bangaren Islamiyya, bayan da suka kammala karatu a matakin firamare. Taron wanda ya gudana a ranar Lahadin da ta gabata ya samu halartar iyayen dalibai da sauran shugabannin al’umma, inda aka mika wa dalibai 12 maza […]

Makarantar Al-Hidaya ta Mararaba ta yaye dalibai

Makarantar Islamiyya ta Al-Hidaya da ke garin Mararaba a Jihar Nassarawa ta yaye dalibanta da suka yi karatu a bangaren Islamiyya, bayan da suka kammala karatu a matakin firamare.

Taron wanda ya gudana a ranar Lahadin da ta gabata ya samu halartar iyayen dalibai da sauran shugabannin al’umma, inda aka mika wa dalibai 12 maza da mata takardun shaida don zarcewa bangaren sakandare na makarantar.

Da yake jawabi a yayin taron, Daraktan Makarantar, Malam Yusuf Idris wanda ya jagoranci walimar, ya ce makarantar wadda ta fara a cikin wani masallaci da ke Unguwar Farin Ruwa kimanin shekara 18, yanzu tana da bangarori daban-daban da suka hada da bangaren firamare da sakandare a bangaren boko da Islamiyya, baya ga bangaren rainon yara da kuma bangaren magidanta maza da mata da ake gudanarwa da dare.

Da ya juya kan matsalolin makarantar kuwa, ya ce burin hukumar makarantar shi ne ta samu babban wuri, kasancewar a yanzu haka tana amfani da tsarin karba-karba ne wajen karantar da rukunin dalibanta da adadinsu ya kai 900. Sannan tana da burin kafa jami’a a nan gaba idan hali ya yi.

Shugaban malamai na makarantar, Malam Aliyu Adam ya bukaci iyaye su rika sa ido da kuma bibiyar karatun ’ya’yansu. Ya ce ala tilas makarantun Islamiyya a Abuja ke ba da hutu a duk lokacin da aka ba da na boko, kasancewar yara na tafiya hutu zuwa yankunansu na asali ba tare da la’akari da makarantun Islamiyya da suke yi ba.

Wani malamin makarantar mai suna Muhammad Haruna, ya ce Annabi Muhammad (S.A.W) ya hori al’umma da su ba ’ya’yansu horo a kan abubuwa uku da suka hada da kaunar Manzon Allah da koyon kur’ani sai kuma kaunar iyalan gidan Annabi.  Saboda haka ya hori iyaye su tabbatar da cewa ’ya’yansu na zuwa makarantun Islamiyya, kasancewar ta nan ne za su fahimci addininsu. 

daliban makarantar sun gudanar da abubuwa da dama a yayin walimAr, ciki har da wasan kwaikwayo. 

An kuma kaddamar da kalandar makarantar ta wannan shekara, inda manyan baki suka saya, a karshe makarantar ta samu  Naira 300,000 da doriya.