Makarantar almajiri ta Khalid bin Walid ta yaye dalibai

Makarantar Islamiyya ta Almajiri ta Khalid bin Walid, wadda gwamnatin tarayya ta gina a garin Benin, Jihar Edo ta sake yaye wasu dalibanta, wadanda suka suka sauke tare da haddar Alkura’ni Mai girma.Taron bikin yayen daliban, wanda aka gudanar a harabar makarantar, ya sami halartar jama’a da dama da suka kunshi hamshakan ’yan kasuwa da […]

Makarantar almajiri ta Khalid bin Walid ta yaye dalibai
Makarantar almajiri ta Khalid bin Walid ta yaye dalibai

Makarantar Islamiyya ta Almajiri ta Khalid bin Walid, wadda gwamnatin tarayya ta gina a garin Benin, Jihar Edo ta sake yaye wasu dalibanta, wadanda suka suka sauke tare da haddar Alkura’ni Mai girma.
Taron bikin yayen daliban, wanda aka gudanar a harabar makarantar, ya sami halartar jama’a da dama da suka kunshi hamshakan ’yan kasuwa da malamai daga kowane sashe na cikin jihar da wajenta.  
Daga cikin malaman da suka hallara har da Ustaz Abubakar Yashe Katsina da Sheikh Ahmad Abu Darda’i daga Kano, wadanda kuma suka yi nasihohi dangane da abubuwan da suka shafi muhimmancin ilimi da matsayinsa ga rayuwar al’umma.
Shehu Ahmad Abu Darda’i  ya yi nunin cewa, “wajibi ne mu nemi ilimi domin Ilimi shi ne ginshikin rayuwa da ci gaban al’umma. Ina kira ga iyaye da shugabanni da a tashi tsaye wajen ciyar da fannin ilimi gaba da taimaka wa malamai masu koyarwa a makarantu. Sannan su kuma yara a kai su makaranta kuma a tabbatar suna halartar ta a kodayaushe, kuma a baiwa malamai hadin kai domin su samu karfin gwiwar koyar da yara, wadanda aka ba su amanarsu”.
Shi kuma Ustaz Abubakar Yashe, a karshen nasiharsa, ya yi nuni da irin ladar da iyaye tare da malaman makaranta za su samu a wurin Ubangiji idan suka tsaya suka karantar da yaran ilimin addini tare da kyakkyawar tarbiyya.