Makarantar Bilal Academy ta Azare ta yaye dalibai 35

Makarantar Islamiyya ta Bilal Academy da ke garin Azare a Jihar Bauchi ta gudanar da bikin saukar Alkur’ani Mai girma ga dalibai 35.Bikin an gudanar da shi ne a harabar makarantar da ke bayan Babban Garejin Azare a ranar din makon jiya a saukarta karo na biyu tun kafuwar makarantar shekara bakwai da suka gabata.A […]

Makarantar Bilal Academy ta Azare ta yaye dalibai 35
Makarantar Bilal Academy ta Azare ta yaye dalibai 35

Makarantar Islamiyya ta Bilal Academy da ke garin Azare a Jihar Bauchi ta gudanar da bikin saukar Alkur’ani Mai girma ga dalibai 35.
Bikin an gudanar da shi ne a harabar makarantar da ke bayan Babban Garejin Azare a ranar din makon jiya a saukarta karo na biyu tun kafuwar makarantar shekara bakwai da suka gabata.
A jawabin Daraktan Makarantar Alhaji Shehu Umar Waziri ya ce, makarantar ta cimma nasarorin da suka hada da daukar nauyin karatun yara marayu 256 a makarantar.
Ya ce, makarantar ta fara ne da karantar da dalibai ilimin addinin Musulunci zalla da daliban da ba su wuce 500 ba, amma yanzu an hada da koyar da ilimin zamani a matakan sashin renon yara da  firamare da kuma sakandare bayan bangaren haddar Alkur’ani Mai girma, kuma a yanzu makarantar na da dalibai sama da 1,500.
Daraktan ya ce a bana dalibai maza da mata 35 ne suka sauke karatu a makarantar, kuma ta shirya karrama wasu fitattun mutane da suka bayar da gudunmawa ga harkokin ilimi da fannonin rayuwa tare da kaddamar da masallacin Juma’ar da ke makarantar.
A jawabin babban bako a wurin taron, Wazirin Katagum Alhaji Sule Katagum wanda dansa Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jihar Bauchi, Alhaji Abdu Sule ya wakilta, ya nuna jin dadinsa ne kan yadda makarantar ke gudanar da karatunta saboda kyakkyawan tsarinta.
Ya yi albishir da hukumar makarantar cewa gwamnatin jihar za ta tallafa musu da na’urorin kwamfuta don habaka ilimin sadarwa ta zamani don tafiya daidai da zamani.
Mutanen da aka karrama sun hada da Galadiman Katagum Alhaji Usman Mahmud da Uwargidan Wazirin Katagum Hajiya Laraba Sule Katagum wadda ita ce uwar makarantar.