Makarantar boyage ta yi bikin nuna al’adun gargajiya

Makarantar boyage International School da ke Abuja ta yi bikin nuna al’adun gargajiya don nuna wa duniya kyawawan al’adun kabilun Najeriya. An gudanar da bikin nuna al’adun gargajiyar ne a babban dakin taron na Hukumar Bayar da Lambar Yabo ta kasa da ke Abuja, a ranar Asabar da ta gabata. Da yake jawabi a madadin […]

Makarantar boyage ta yi bikin nuna al’adun gargajiya

Makarantar boyage International School da ke Abuja ta yi bikin nuna al’adun gargajiya don nuna wa duniya kyawawan al’adun kabilun Najeriya.

An gudanar da bikin nuna al’adun gargajiyar ne a babban dakin taron na Hukumar Bayar da Lambar Yabo ta kasa da ke Abuja, a ranar Asabar da ta gabata.

Da yake jawabi a madadin shugaban makarantar, malamin da ke kula da fannin bayar da shawara da kirkira, Mista Ituen Alfred ya ce sun shirya bikin ne don su nuna wa daliban muhimmancin al’ummar da suka fito daga cikinta.

“Najeriya muna da al’adun gargajiya masu kyau kuma abin koyi saboda haka muke so mu nuna wa dalibanmu muhimmancin al’adunsu sannan mu nuna wa duniya cewa kabilun Najeriya suna da kyawawan al’adu,” inji shi.

Ya ce baya ga kayan sanyawa na gargajiya, daliban sun yi bayanin abincin gargajiya iri-iri da tsarin masarautu da kuma koyar da harshen kabilu daban-daban. Ya ce mahalarta bikin sun karu da abubuwa masu yawa da suka kunshi al’adun kabilun Najeriya.

Dangane da harshen Larabci kuwa, malamin ya bayyana cewa daliban sun gudanar da wasan kwaikwayo da harshen don su nuna wa duniya muhimmancinsa. Ya kara da cewa harshen Larabci yana da muhimmanci a makarantar saboda haka ne makarantar ta sanya shi cikin manhajar karatunta.

Da ya juya kan kyaututtukan da aka raba wa daliban, sai ya ce daliban da suka nuna kwazo da bajinta sun cancanci yabo. Ya ce shi ya sa makarantar ta ba su kyaututtuka masu yawa don kara musu kwarin gwiwa kan karatunsu.

daliban makarantar sun gudanar da wasannin kwaikwayo da harsuna daban-daban kuma an bayar da kyaututtuka ga daliban da suka yi fice a fannin lissafi da harsunan Larabci da Ingilishi da Kimiyya da Fasaha da kuma kyaututtuka ga malaman da suka fi nuna kwazo.