Makarantar Darud Da’awatil Islamiyya ta yaye dalibai 36

Makarantar Darud Da’awatil Islamiyya da ke Unguwar Sabo a Ibadan ta yaye dalibai 36 maza da mata da suka haddace Alkur’ani Mai girma da kuma Izifi 10. Shugaban Makarantar, Ustaz Mustapha Abdulmalik ya ce duk da  wannan nasara da makarantar ta samu wajen koyar da ilimin addinin Musulunci ga ’ya’yan Musulmi, akwai wadansu iyayen yara […]

Makarantar Darud Da’awatil Islamiyya ta yaye dalibai 36

Xaliba Asma’u Abdulrazaq wacce ta haddace Izifi 60 na Alqur’ani

Makarantar Darud Da’awatil Islamiyya da ke Unguwar Sabo a Ibadan ta yaye dalibai 36 maza da mata da suka haddace Alkur’ani Mai girma da kuma Izifi 10.

Shugaban Makarantar, Ustaz Mustapha Abdulmalik ya ce duk da  wannan nasara da makarantar ta samu wajen koyar da ilimin addinin Musulunci ga ’ya’yan Musulmi, akwai wadansu iyayen yara da suke yin sako-sako wajen biyan kudin makaranta da ake amfani da su wajen biyan albashin malaman makarantar.

Malamin ya fadi haka ne a ranar Lahadi a wajen bikin yaye daliban makarantar na bana, wanda Marafan Ibadan, Alhaji Audu Lawal ya shugabanta.

Dukan dalibai 36 sun samu kyautukan Alkur’ani da suturu da agogon hannu da kudi masu yawa da wani dan kasuwa, Alhaji Umar Ajiya ya bayar.

Ustaz Mustapha Abdul Malik ya yi nasiha a kan amfanin koyar da yara ilmin addini inda ya ce, “Karatun Alkur’ani da ilmin addinin Musulunci yana taimakawa kwarai wajen sanin yadda ake bautar Ubangiji kuma yana hana aikata ayyukan sabon Allah. Idan yaro ya koyi ilimin addini to kuwa yana da wuya ka same shi a cikin masu shaye-shayen miyagun kwayoyi da ke kai su ga sace-sace da sauran miyagun ayyuka.

Ya ce iyayen dalibai 235 ne kadai suke biyan kudin makaranta a kan kari daga cikin iyayen dalibai 535 na makarantar. Sauran daliban 300 da iyayensu ba sa biyan kudin makaranta sun hada da 51 ’ya’yan malamai da 50 ’ya’yan masu rauni da 120 ’ya’yan marayu da 79 ’ya’yan wadanda suke guje wa ranakun biya, suna komawa bayan an biya kudin makaranta.

Da yake nuna farin ciki da irin nasarar da makarantar ta samu a bana, Marafan Ibadan ya yi kira ga iyaye su daina wasa da ilmin addinin ’ya’yansu.

Alhaji Umar Ajiya wanda ya bayar da kyaututtuka ga dukan daliban da aka yaye, ya yi wa Aminiya bayani cewa, “Wannan muhimmiyar kyauta ce da Allah (SWT) Ya ba wadannan yara da suka sauke tare da haddace Alkur’ani, wanda hakan ne ya ba ni sha’awa wajen yin amfani da dukiyata domin taimaka wa makarantar da dalibanta da zai kai ga samun shugabanni na kwarai a nan gaba.”